Share this page
4 / 5
nemi manyan babys ynxu gashi kana yi ma yar cikinka rantsuwa ita kuma sai masifa take maka ynxu ina girma?babu babba wani abun ma sai taga gadon kwananka Adams yayi murmushi yace wannan ra'ayinka ne kawai niko ina son in auri yarinyar dan na more sadakina da kyau Maska yace in ka samu big girl shine zaka more sadaki Adams yace mu bar zancen haka Maska yace kai dai ka sani yaushe zan bar yar yarinya ta juyani? ai ni in babbar ce ma sai ta raina kanta in tace zata kawo min iskanci Adams yace in baka sonta ba ba in kana sonta komai zatayi maka zaka jure sai kaga karamar ta juya ka babbar bata juya ka ba,tsaki Maska yayi sannan yace baka gama sani na ba har ynxu don ina son mace tayi kadan na jure iskanci, sannan ya mike ya tafi Adams na mishi dariya. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Muna zaune a dakinmu muna aikin gyaran katunan bikin su Mami yau saura kwana takwas bikin kuma yaune su yayanmu zasu iso shine babban abokin ango kuma babban yayan Amare,na dubi Mami nace ya kan Badarawa,Malali,da Unguwar sarki ya kamata muje dan yan skull zamu gayyace sosai mun dade bamu hadu ba mami tace haka ne yi sauri mu biyama Amira,tare muka shiga gari sai magriba muka dawo sai dai in lokcin sallah yayi mana mu tsaya muyi,shirye shirye sunki karewa saboda wasu abubuwan bada su Sa'a zamu hada ba walima ce kawai tare sai Sisters day da su Anty Mariya suka shirya a gidan yaynmu in sun iso a Yakubu Avenue amma mu zamuyi lunchn sannan angwaye sun shirya dinner,mun dawo mun sami yaynmu ya iso saboda gidansu sai an gyara da yan share share gurin su Sagir na sami lbr isowarsu sai ga kuma wayar Adams yana ce min sun iso ynxu suna tare da ango nace to sannu da zuwa me zan shirya maka?yace komai ma nace to an gama nadai daure ne nayi wannan maganar dan kar ya ce ban yi murna da zuwansa ba amma zahiri hankalina yana kan yayanmu da kuma masifar son ganinshi,nan na dan yi girke girke na san Adams na zaci zan sameshi tare da yaynmu a dakin yaya kabir din ina sai shi kadai na samu dan haka shi kadai yayi ta surutanshi Adams ya dubeni kin kara cika fa yar gidana ina son Maska ya ganki shi da yake cewa zan auri yar cikina nace um! Sama sama mukayi hira sannan na koma gida shi kuma ya nufi gidan Nasir har ramar lalle banga yaynmu ba ko anty mimi ban gani ba mu da yake gidansu Amira mukayi namu lallen su kuma gidan Anty Hadiza sukayi,sisters day shine abu na farko da kamar kar naje mami tace in banje ba bazata ba dole tasa nace to zanje,da yake dama gurin babana naje na amshi kudi na shiga kasuwa materials da lace sai da naga karshen tsada na sai mana takalmi da jaka ai fdi ma bata bakine ganin abin rabawa na buga jaka na buga bokitai na roba sai na buga agoguna har fada mama tayi min wai naje ina amso kudi masu yawa haka shi kuma ya biye min,nace to mama kiyi hakuri ni ban yana cewa in basu isa ba zai kara min wasu wai dan ni kadai yake neman kudi,mama tayi tsaki ta shige daki mu da Amira ba muje shirya gurin da zaayi sisters day din ba dan gudun rikici sai bayan an gama komai an soma kai kawaye sannan muka shirya,jan material dan dubai shi na dinka riga da siket nasa duk yanda mutum ya kai ga hassada ba zai kusheni ba a wannan rana takalmi da jaka bakake nayi amfani dasu kafin amira ta gama shiri na shiga gidan mu na fito wata mummunar faduwar gaba naji sanda na hangi yaynmu a kofar dakin yaya Kabir shi da Nasir sanye yake da wando jeans baki da riga fara ta kama jikinshi kyau annuri ne ke fita a fuskarshi yana da kyau na karshe fatar shi ta kara zama smooth giran gashin shi kuwa abin birgewa ne,kamar na juya sai na dake tunda bai ganni ba gara na nuna ban ganshi ba sai da nazo daf da su sai Nasir yace kai Iman wannan dauke kai haka?na juya da sauri ango ban ganka ba ne,na isa wurinsu na dubi yaynmu wanda yayi wani kicin kicin da fuska nace sannu da zuwa yaynmu kunzo lfy?a ciki yace lfy duk sai naji ba dadi dan haka sai nace Nasir a kirata ne?yace a'a ba gurinta nazo ba sai na wuce ciki,ganin yaynmu sai tsohon ciwona ya tashi wutar sonshi ta soma ruruwa a cikin zuciyata ranar dai sai a hankali mun isa gidan yaynmu sai naga ma ashe duk yanda suke bada lbr haduwar gidan ya wuce nan gefen da ake sister day lambu ne yanda suka shirya yayi kyau Amare kaya iri daya suka sa tunda muka zauna bamu tashi ba sai da aka soma liki sannan ne na shiga nima na bada tsoro da kudi na fito,anty mimi tayi kyau sosai cikin farin tattausan leshinta rigar fitet ce don haka cikinta ya dan fito dan das daga mun hada ido sai ta dalla min harara har Amira ta lura da ita tace ke kefa matar can take harara nace tayi ta gama abinda yasa ma bata neme ni da rigima ba dan tasan yanxu bama shiri da mijinta ko ince an samin rana shiyasa Amira tace haka ne kam,wayata ta soma ringin na duba sunan yaynmu na gani gabana yayi mummunan faduwa na dauka yace ina jiranki a falon gidan nan cikin in ina na ce ban san hanya ba ki tambaya sai ya kashe wayar na dubi Amira kinji yaynmuda rikici ko wai na sameshi falonsu bayan dazu da ya ganni sai ya wani daure fuska Amira tace kije mana nace to ai tana kallona matarshi Amira ta ce to zauna ina ruwana,na mike na nufi hanyar waje nan na kirashi nace ban gane hanyar ba gani a gurin bakin gate,yace ni kenan kike nufin in zo ko?sai ya kashe,gun mai gadi na nufa nace mishi dan Allah ina kofar falon,ya nuna min sannan na nufa sanyi da kamshi da kuma laushi su naci karo dasu ina shiga falon,yana zaune yana shan coke na isa gurinshi har ya canza kaya daga bakin jeans zuwa blue da yar shirt,na dan rusuna gefenahi yace tashi ki zauna kan kujera na tashi nabi umarninsa yana kallona kamar hoto ko TV yana shan coke na gaji kar matar shi tazo sai nace gani yace na ganki sai yaci gaba da abinda yakeyi da danne dannen waya,can sai yace ke kamar ni nazo garin nan ace ki gagara zuwa ki gaisheni?sannan da muka hadu sai kika wani dauke kai ke kin girma wai shekarar ki nawa ne?nayi shiru dake nake na dubeshi fuskata a daurena kauda kai,ba kya jina nace sha takwas yace to me na miki kika kasa gaidani?nace ban gane kaba ne shiyasa shi yasa kika manta dani ko?baki taba yi min waya ba tun da natafi me yasa?nayi shiru can nace to kayi hakuri,aikin ki kenan bada hakuri to na hakura menene shirye ahiryen na ki bikin?na dubeahi ni bani da wani shiri yace ki dai fada tun da wuri kinsan ance mai kwarmin ido da wuri yake sa ma kuka nine uban Amarya kuma nine abokin ango,haushi ya kamani nayi kicin kicin yace to menene na bata ran kamar ba ke kika zabi mijinki ba?sai ya canza magana baba kwana biu ban kirashi ba kuma tun da nazo banje ba amma zanje mu gaisa nace dama kana kiranshi ne? sai ya share zancen,kun zan jarabawar?munyi,to Allah ya bada saa amin ina yan waige waige yace me kike kallo ne ki saki jikinki gidana kike ba na wani ba ni ko yaynki ne,Amira da Mami sai doko min waya suke ina cewa gani nan yaki sallamata,har suka tashi sai ga mutane na mike da sauri harara ya sakar min ba shiri na koma na zauna a raina nace kai dai kana shaawar kowane biki sai ka sani a problem,sunyi mamakin ganina sosai fuskar anty mimi a kaina,Nace don Allah zamu tafi shi kuma sam ya ki sai da yayi raayi sannan yace to wa zai kaiku?nace mashin yace bana son kina hawan mashin fa nace to nabi motar Nasir ni da Amira,to sai yaushe nace ai yanzu kuna nan zamu yi ta gaisawa ko yaushe yace shi kenan,washe gari lunchn tun safe ba hutu sun tafi gyaran gashi ni kam da bani kona gashi sai na tafi kitso biyar daidai kowa ya shirya sai mu kawaye da Amarya ake jira dan har an soma dibar kawaye bayan na shafa mai sai inner wears na dakko less wanda ya amsa suna less kalarshi ba zaa kirashi milk ba kuma ba zaa kirashi yellow ba shi kuma ba light brown ba yana dai tsaka tsaki na saka shi sannan nayi shafe shafe kai ni kaina nayi mamakin kyan da nayi sai da na gama shiri tsaf sannan na fito kai Iman inji Mami gsky ko ni amarya kin fini haduwa gsky cire inji Mami nayi murmushi nace ba wani kyan da nayi,kafin tayi magana sai ga su Amira da sauran kawaye kowacce sai da ta raina kwalliyarta ynxu burina inga yaynmu shima inji ta bakinsa mun fita harabar gidan mu yan mata ne tsantsam nan kallo ya koma kanmu Adams ne tsaye suna magana da sauran abokan ango yana hango ni sai kawai ya wani washe baki yana kallona amira tace iman ji mutuminki nace naganshi share kawai,ya iso gurinmu Amarya gsky ba tare da ango zamu kaiku ba sai dai ya haura ma kanshi daga baya,Mami tace saboda me kace haka Adams?Ya nuna ni yace ga yar gidana da Amira ku zauna tare a motata don ni ne zan tuka ku na juya zan mishi magana sai wata masifaffiyar hadaddiyar mota ta kunno kai harabar gidan duk mutanen dake gurin sun raja'a ga ganin motar, baka ce wuluk haka gilashin ta ni kam shashancewa nayi ina duban motar dan tunda nake ban taba ganin mota irin wannan ba,Adams ne yace sai Maska dai dai lokacin da yayanmu ya fito cikin wata shadda galila yar gaske sai maiko take,hatta numfashina sai da ya dauke na yan dakiku sannan ya dawo daga nesa damu yake amma kamshin sa har gurinmu,Adams ya ce sai Maska yaynmu ya dago mishi hannu ya mishi alamar yana zuwa 'yan mata suka bishi da kallon birgewa yayin da wasu suka kyasa A hankali nayi ajiyar zuciya sannan nace Adams kun damu mu fito ga mutane ba'a gama kwashe su ba ya za'ayi mu tafi?ya ce to ynxu ya za'ayi kenan? Amira tace don Allah ku gama kwashe su mana sauran abokan suka ce to,yaynmu ya kuma fitowa gurin motarshi ya nufa Adams ya bishi ya bude mota suna magana da Adams ko me suke cewa oho?sai Adams ya dawo shi kuma ya shiga cikin motar sai kuma ya fito ya dubi gurinmu da hannu ya yafito ni gabana ya fadi nace Amira yayanmu yana kirana mami tace karki dade fa banko iya magana ba na nufi gurin motar sai na samu kaina da canza salon tfy cikin isa da kasaita na iso gurin motar gefen kusa da dryva ya bude dan haka sai na zagaya nayi magana sai naji yace shigo ba musu na shiga kamshi da sanyi sukaimin sallama cikin isa da jan aji ya tashi motar ba tare da ya dubeni ba cikin gwaninta ya fusgo motar da gudu sai da muka hau titin Bako Road sannan ya kara sautin wakar p square cikin wakar su ta no one lyk u,na jingina da kujera ina sauraro wakar na zata gurin lunchn zamu je sai fa naga mun dau wata hanyar ban ankara ba sai gamu gaban gidan yaynmu dake Yakubu Avenue gabana ya fadi sannan tsoro ya bayyana a fuskata yaynmu ya dube ni sai ya fito da waya yana yan danne danne shi ban sani ba ashe hotona yake dauka ban sani ba,na rufe wayar sannan yace bisimillah mu shiga nace me zan yi yaynmu?kasan fa gurin Lunchn zamuje,yace nima bazaniba dan haka kema ki hakura da sauri na dubeshi cikin damuwa nace mami ba zata ji dadi ba fa yanda muke da mami ban kyauta mata ba,dubana kawai yake sannan yace to mimi taje mana ni dake dan haka ynxu ma ni yunwa nake ji mu shiga ki min abinci na dubi fuskar shi ba alamun wasa amma duk da haka sai da nace bai dace matar gidan ba ta nan ba na shigar mata gida ya daka min tsawa gami da cewa tsaran ki ne ni kike yi min musu?bayan mun shiga ya tsaya da motar na fito shine a gaba ina binshi a baya har falo ya zauna nace inane kicin din bi nan ya nuna hanyar,na tafi komai na kicin da ake bukata akwaishi dan haka na shiga aiki gasky na raina tsaftar matar gidan banyi karambanin gyra mata kicin ba nidai nayi iya aikina farar taliya da miyar kwai da hanta nayi mishi a gabanshi na jera komai na koma na zauna ya dubeni zo mu ci kai kawai na girgiza dai dai lokacin da naji ringing a cikin jakata na ciro wayar har ta katse na duba 11 miss call na duba su Mami ne da Adams na dubi yaynmu dake faman cin abinci nace su mami na jirana ya dubeni kin san bana son nacin magana ko?ya kamata ki rike wannan ya cigaba da cin abincin shi sai da yayi dam sannan ya shige dakinshi wanda an rubuta master bed room a jikin saman kofar dakin da yellow din kala kamar minti biyar ya fito zo muje Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 A ranar haka muka yi ta yawo a gari dan mugunta har magariba kuka ne kawai banyi ba dan haushi wai ace biki kamar na mami bana guri ai da takaici gashi ya amshe wayata ya kashe na rasa irin wannan ikon, gidan shi muka koma ya tafi masallaci ya barni wai nayi sallah cikin dardar na zauna sai bayan ishai ya dawo ko sallar ma banyi ba ya kuma daukata ya shiga gari sai tara ya maidani gida lokacin an tashi daga lunchn din dan haka dakinmu na wuce na fada gado ko da mami ta shigo da fushi ganin ina kuka sai ta sakko tana tambayata menene?cikin kuka nakece mata yayanmu ne ya daukeni sai yawo yake dani ya hanani zuwa gurin lunchn dinki tace ba komai kila shima yana da dalili nace wanne dalili?shidai burinshi ya ga raina a bace nan dai ta shiga lallashina. Washe gari aka daura wasu mami aure, da daddare aka kai mami gidan Nasir dake unguwar sarki tun fara bikin sai yaune muka sake nida Adams dan yayanmu ya kasa ya tsare yaki barina na cashe ashe shi yana can suna yinta da anty mimi yace ba zata zo ba ita kuma tace sai ta zo ya gama shirinshi tsaf ta taso har gun mota ta biyo shi tana cewa sai taje,ta shige mota itama tata kama murfin motar yace sake min tace sai fa naje yace ke kina fa cin darajar cikin jikinki ne bayan haka dakin san ina fada kina fada ba zata yiwu ba amma zaki haihu ba zan dau wannan iskancin ba wata macen arziki ce zata bar gidan aurenta karfe goma kuma bata san sanda za'a tashi ba to tunda lallashi baya miki zan biki da zafi yaja murfin motar ya rufe sannan yaja motar,muna tsaka da fira sai ganinshi mukayi tsakiya suka sani shida Adams,Adams ya dubeni mun zata ba zaka zo dinner kanwa ba?yace kasan mai iyali saida na lallameta tayi barci Adams yana yayi kyau muma dai Allah ya kaimu ga jarawa ,ni kam kumallon ya motsa don haka duk haushi suka bani Adams ya dubeni yar gidana kina gaya min kince zakuyi lunchn da mene?nace sai mun zauna dasu Amira menene na sauri Adams da sauran lokaci fa,yace ba wani lokaci gara ki fada min don in na tafi sai ana sauran kwana daya biki zanzo in nasan komi tun yanzu zaizo da sauki,na dubi yaynmu wanda yake ta aikin danne dannan waya tamkar baya jin mu nan ko yana sauraren komai nace to kafin ka tafi zamuyi zancen, gobe fa zan tafi cikin kosawa da maganar nace to baga waya ba Adams yace to shi kenan ya canja zancen da hajiyata tana son jin muryarki bari na kirata ku gaisa,nace haba dai daren nan?ka bari sai da safe yace to na bari kinsan ni ba dai cikin gimbiya ba nayi dariya nace to Allah yasa ka dore ba sai naje gidan ba a canza min yace haba aini din nan ko bawa kika samu kinsan yanda nake son ki kuwa?kin san nutson da nayi a kogin kaunarki?in da ace kinsan yanda jiki da jijiya da bargo da kashi da tsoka........kai yaynmu ya daka tsawa ya cigaba haba Adams ka tasa yarinya karama kana wannan kauyancin?ai wannan soyayyar dace in kana sonta idonka kadai ya isa sheda ba sai kanata wannan batun ba ka gane wannan ai yar da girma ne da ga ni har adams kallonshi muka tsaya yi sai da ya gama sannan yace Maska kai komai naka daban ne kana da hali irin na masu girman kai...yaynmu ya daga mishi hannu ya isa yi tayi,Sai karfe sha biyu muka tashi daga dinner washe gari muna sallama da Adams yace sam bikin nan bai min dadi ba,dan naso muyi hotuna muyi hira mai isarmu amma haka bai samu ba nace kar ka damu tun daga waya maganar hoto sai na shiga na miko maka munyi sallama nabashi hotuna ya diba son ranshi mun rabu akan sai naji shi a waya haka muka rabu,bayan gama bikin mami yaynmu bai kuma damuna ba sam gaisuwa ke hada mu sai dai da naje gidan babana ne yake cewa yayanmu yana zuwa yana gaisheshi har yazo da mai dakinshi ya yabeni tare da fadin kirkinshi,ranar ma muna zaune a falon babana dani da Anty Maijidda sai ga yaynmu sun gaisa da anty maijidda sannan na gaisheshi anty tace kije ki kira babanki na tashi na dauki dan kwalina naje na sanar dashi,yana fitowa naga ya soma fara'a ganin yaynmu suka gaisa sannan yace yazo ne ya mishi sallama dan gobe zasu koma sai kuma nan da wata hudu lokacin bakina da abokinshi babana yayi mishi godiya gami da sa albarka sañnan yace ga kanwar ka nan dama ta dameni wai nayi sallar magariba na kaita gida don haka sai ta tashi ku wuce,na ce sai gobe zani,babana yace a'a ni kinga gobe kwatano ma zamu,na soma shagwaba nayi takwa takwa da fuska nace nidai to ai baka sai min abinda kace ba yace me nace zan sai maki? computer yaynmu ya harareni na kauda kai babana yace to in na dawo ranar sati monday sai na sai maki shi kenan?nace eh yace to uwata maza tashi yaynki na jiranki na mike ina fadin ko kana korata ne?ba zan sake zuwa ba suka sa dariya shida anty Maijidda yace wane ni na kore ki ban isa ba nayi kadan anty tace naje daki na dauki kayana na dauka tace na gaida mamana,tunda muka dau hanya ni da yayanmu ba wanda yayi magana can yace gobe zamu koma sai kuma bikinki na dubeshi to Allah ya tsare hanya na fada cikin karfin hali,tunda muka zo gida muka samu haj yaya a harabar gidan na soma tsuma,cikin tsoro nace gasu haj,to menene yace yana fakin na fito da ido suka bini shi kuma ya nufi gurin su ni kam gida na wuce,yace haj daga ina?ta daure tace nan makwafta muka shiga barka ta cigaba matarka tana jiranka ashe kai kuma kana nan kana yawon banza daga ina kake?daga tudun wada,gurin wa?gurin baban iman ta kuma dubanshi muje ciki gani nan tana mamakin halinshi shi mutum ne wanda baya shakka ko karya komai zai fada in dai gsky ne zai fada sai dai a mutu Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Haj yaya fada take tana karawa tace eh dan shashanci matrka ta na nan tana jiranka kai kuma ka tafi gidan kanin ubanka yace to haj dan naje munyi sallama shine damuwa?to kiyi hakuri ta dan sassauto kai baka da tunani yanzu in kai wanine yaushe zaka bar Adamu abokinka ya nemi yarinyar nan ga kannenka?yace wadanne kannen kuma bayan sunyi aure?ko ba ma haka ba ai matar mutum kabarinsa....tace nasan haka amma ni na sha alwashin sai na hana auran Iman da Adamu in dai ina numfashi yanda bana son ta rabeni kaima bana son ta rabi na kusa da kai kaf yayana wacce ce ta samu mai kudi dan mai kudi kamar Adamu?babu dan haka itama ba zata aureshi ba,sororo yayi yan dubanta sai da ta gama sannan yace to haj ke me zakiyi akai?dan Allah ki bar maganr nan,tace nasan abinda zanyi kai dai tashi ku tafi Allah ya tsare hanya kana can zakaji lbr,yaso yayi mata nasiha gami da shawara amma sai taki ta hau shi da fada,dan haka sai yace to haj zan wuce ba zan samu dawowa da safe ba saboda sammako zamuyi ta kano zamu tashi sakon ki gobe in Kabir ya kaimu kano ya dawo zaije banki ya amso maki kudin,ta ce zaka kara min dubu talatin akan na da yace ba komai zai kawo maki ina Mimin mu wuce,haj tace tana gidansu, ya dubi haj wa yace taje jiya fa can ta yini haj tace ai ba'a gajiya da gida ka dai biya ka dauketa yace Allah ba zan biya ba tunda ban aiketa ba in ta dawo shi kenan in bata dawo ba ta zauna,Haj ta dubshi gara da ka nuna na gani dama ta kawo min kara kana wulakantata son ranka yace haj ni kinsan abinda take min ne? bata san kula da miji ba bata san darajar miji ba bare yanda zatayi biyayya son jiki bata iya girki ba,ni nasan ina da mata amma sai na fita yawon gidajen cin abinci,tace to ai komai dan lallashine yace wane lallashi ne ban mata ba amma nasan maganinta zata gane bata da wayo,ya mike mun tafi haj tace Allah ya tsare kar dai ka yarda naji wata magana. Sosai su haj yaya suka hau shiga malamai duk wai dan araba Iman da Adams ko ina ruwansu oho?nikam bansan me suke ciki ba,muna hira da Adams yanzu na sadaqar shine mijina kuma na hakura shirye shiryen dasu mama keyi na bikin nan ba dama har dubai su mama sukaje da anty yagana ga wasu jike jike da suke faman dirkamin bansan ko na menene ba sunce ma in saura sati biu bikin zamuje maiduguri a gyarani bansan gyaran da za'a min ba tunda dai nasan nima ba dan laifi baka ce amma ba bakikkirin ba hancina ba dogo bane kuma ba gajere ba bakina mai dan fadi da sirrin lebuna idona farare kal kuma ba kanana ba ne gudar gadar ne musamman ma in na tsorata kamar yanda naji ana cewa,sai muryata ni kaina nasan ina da murya mai shegen dadi game dajiki nasan akwaini dan kasa da sama ba matsala mutane da yawa jikina ke rudarsu ba wai so ba to ban san gyaran da suke nufi ba.Yau ni da Amira gidan mami muka je dan shirye shirye bayan munci munsha sai muka shiga abinda ya kawo mu can nayi tsaki gara mu tsaida magana don sati na sama zamuje maiduguri mami ta ce yin me?na dan tabe baki wai gyarani za'ayi har ma dariya abin yake bani mami tace ba sauki nace dan Allah wai gyaran menene? sukayi dariya Adamu zai baki amsa gabana ya fadi nace kuyi min bayani mana,mami tace kefa mukayi magana dake kwanaki nace ni duk ynxu tsoron Nasir nakeji kikace ke bakya tsoron Adams to zaki ji tsoron nesai kin shiga hannu,mu dai ynzu mun ketare sai ku, gashi har wani gyara za'ayi mashi Amira ta yi dariya tace nidai hankalina kwance nace zaima tashi ne na dubi mami nace da wuya ko?mami tayi dariya tace bance ba sai ta kuma kwashewa da dariya nace muguwa tace ba komai zan dai ji jiki ne.Tin ana sauran sati uku biki Adams ya aiko min da katuna ban taba ganin kati mai kyau irin wannan ba tunda naga katin sai jikina yayi sanyi na shiga daki sai kuka,babana ya kirani yace duk abinda nakeso na fada nace komai yayi min yayi,yayi yayi muje kasuwa na zabi kayan daki da kaina naki,yan uwan Adams sun kawo kaya akwatina saiti biu sai naga ma kamar ba gaske ba,yau juma'a maiduguri ta dauka tun da muka je sai aka shiga gyara ni daki aka ware mani nida mai gyarani nan gidansu anty yagana satinmu daya mun dawo ana saura sati daya bikinmu ni kaina nayi mamakin kaina dana dubi madubi sai kace bani ba yanzu kam na yarda gyara na mukaje dan nayi kyau san da na dawo su Amira sunyi nisa da rabon kati duk wanda ya kamata sunkai mishi batun yan gidan mu su haj yaya sunsha mamaki ganin shirye shiryen da ake ganin gyare gyaran da ake min ya kara firgita su gashi boka ya masu alkawari za'a fasa auren gashi har lefe yazo mai yawa koda mama tace sujesuga kaya ba kunya sukaje don gulma ganin kaya da gwala gwalai sai jiki ya kuma sanyi waya haj yaya tama laure akan tazo da magana bayan sun shiga uwar daki haj yaya tace laure zama bai ganmu ba kaya tun ana kirga zannuwa da nazo hamsin sai na daina ganin gwala gwalai sai hawan jini na yaso taso ya tashi ba arziki na fito daga dakin haj laure tace ynxu menene abinyi?yaya tace innaga gurin malamin nan zamu koma.... Adamszaune gaban malami ko nace boka ya dubesu kin cika gajan hakuri an daura auren ne?suka ceaah yace to na gaya muku ba shi ne mijinta ba zaa ba wani ne adakaa zaku sha mamaki kuje ku nutsu nan da kwana uku zakuji lbr ya canza rauhanai sunanan suna aiki yanda ya kamata nan suka yi godiya suka fita.Yau sauran kwana uku biki zaune nake akan kujera a wani daki gidan anty yagana nan muke nida kawayena yar borno wacce ta gyarani a maiduguri itace ta zo yau danmin lalle na musamman an zana shi hannu da kafa an ratsa jan rani dama kafin a fara sai da aka

Chapter 4 of 5