Share this page
3 / 5
har kasuwa ya sameni shi da wani Ibrahim ban san wanda ya nuna musu ni ba sai dai ganinsu nayi nace miki har kuka yayi gabana yanzu kiyi hakuri ki zo muje suna falona ku gaisa,mama ta ce cikin fushi Alhj Mukhtar na taba yi maka musu?yace a'a tace to tin da kaji nace ba zani ba itama ni na haifeta ba zata ba to,ko kukan jini yakeyi ba zamu ba,yanzu ne ya san damu?ba zan iya ba wllh in kuma ya matsa min sai na maka shi kotu da sauri na dubi mama kalmar ta bani mamaki sam ban taba tunanin mama tana fushi haka ba hawaye ya soma zarya a kumatuna sam ba zan so haka ba Alhj da shima mamaki ya hana shi magana sai ya mike ya fita falon shi ya sami babana da yaya Ibrahim hakuri ya basu gami da ce masu su je su sami kawu malam can kuwa suka tafi kawu malam ya jima yana yima babana nasiha sannan ya ce je gobe ya dawo suje unguwar Rimi Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Misalin karfe biu saura kwata 1:45,zaune nake kan sallayar da nayi sallah na jima ina adduoina game da matsalolina, mama dake kan kujera ta dubeni Iman ynxu ya zaki hada lesson da comp school din na ce nifa mama ynxu duk basu dameni ba krt ma ya fita daga raina mama ta kafa min ido sannan tace to me zakiyi in baki krt ba?nayi shiru ta saka salati ku jimun yarinya aure kike so ke nan ko?nan ma banyi magana ba tace shi kenan kudina sun huta sai ki fito da mijin ko,na dubi mama nace bafa dan haka dan haka bane dan....sai kuma nayi shiru,yi min magana dan menene?nace dama wani abokin yaynmu da yake can England yake sona yace kuma a can zamu zauna can zanyi karatuna,mama tace Alhj yayi min maganar shi yo koma zakiyi krt ai dai sai da sakamako mai kyau ko?nace to wane ma lesson zan shiga,mama tace ga wata nan ramat road ki shiga tunda an kusa fara jarabawar ina gama salamat tsohuwar makarantarku zaki zana jarabawar a can,nace yauwa dama yafi,...Alhj ne yayi sallama mama tace lfy Alhj?na ganka da rana yace lfy lau ya dubeni nayi mishi sannu da zuwa yace kuzo Habiba ke da Iman ku sameni a dakina gabana ya fadi mama tace in fa baban Iman ne ba zani ba yace ina dai jiranku,falon cike yake da mutane Alhj ne a kujerar bakn kofa 2 sitter sai kawu malam can gefe na gane yaya Ibrahim da kuma babana sai wasu mutane uku da ban sansu ba nan da nan mama ta dunke fuska kusa da Alhj ta zauna nima na zauna kasa gefen mama,sai baba yace uwata zo nan kusa dani mana ,na dubi mama sai naga bata kalleni ba dan haka sai na nufi babana kasa na zauna ya jawo ni kaina ya dora kan gwiwowinshi naji wani irin muguwar soyayya irin ta da da mahaifi na ratsani kawu malam ne ya soma magana Habiba ga uban Amina ya zo bada hakuri akan irin kuskuren da ya aikata a can baya,mama tace ai bai min komai ba,babana yayi karfin hali yace haba Habiba nasan nayi maki kuskure dan Allah ki yafe ni nasan baki da ruko habiba,mama tace ai ni Idris dan ka sakeni ba laifi kayi ba tunda halas ne sannan Allah ya bani wani mijin wanda yafi ka komai nima sakamakon hakurina kenan,na dubi mama banji dadin maganar data fada ba babana akafi?na kuma gyara kwanciyata a jikin shi ni ina sonshi nace a raina,kawu malam yace yanzu dai yace ki yafe mashi babna yace yauwa nidai kimin aikin gafara mama tayi shiru sauran mutanen sukayi tasa baki mama tace meyasa sanda ya zalunceni ba wanda ya bada baki sai yanzu da ya milla da kanshi zaizo ya wani ce wai na yafe mishi,kai Idris kai ne mutumin da banyi tunanin yi maka afuwa ba,ta soma hawaye kai ne ka aure ni tun baka da komai kai ne ka fara sanina ya mace kai na fara haifa ma 'ya amma daga karshe ka ce na tafi da yata kai kafi son 'ya'ya maza daga tsatson fati ka manta?dan haka ynxu ma sai kaje gurinta Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Tawa Tasameni 2-02 Posted by ANaM Dorayi on 08:27 PM, 03-Jan-16 Under: TAWA TASAMENI __________NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI________ Tunda muke da kai ko ince tunda muka rabu da kai ka taba kawo daidai da pant aba Iman,Alhj yace kiyi hakuri Habiba ya wuce kice kin yafe masa,mama tana kuka Alhj da sauran mutane ma suna bata hakuri kawu malam ya soma mata fada to tunda duk nan ba mu isa ba shi kenan karki yafe ko Allah ana mishi laifi yana kuma yafewa bare ke,ganin ran kawu ya soma baci sai tace shi kenan ya wuce ya shiga godiya yace Alhj Mukhtar kaima na gode da irin rikon da kaima uwata Allah ya saka da alheri ya dubeni uwata ynxu wacce makaranta aka gama?ko shirin aure akeyi?na boye fuskata a gwiwarshi,Alhj yace sun kammala sec bara to paper din tata batayi kyau bane shine zata gyara sannan asan abinyi, babana yace to batun miji fa? Alhj ya ce eh akwai wani Adamu abokin Abdulrahim tare suke sana'ar tasu can a England shi nake zaton take so,amma sai mun gama bincike mutumin Ghana ne ina da abokin kasuwanci a can binciken ba zai bamu wahala ba tunda Abdulrahim yace min game da halayen Adamu babu matsala karatun ma yace a can zatayi shi ne nace ya nemi iso gurinta,babana ya dubeni uwata kina sonshi?na kada kai alamar eh sannan na boye fuska ina kuka dan na san ba shi nake so ba,babana yace Alhj kaga wani sakarci?wai kuma kuka take yi,mama dama tuni ta tafi nima na tashi zan tafi babana yace uwata wai yaushe zaki zo mana kwana biyu ne?na ce sai na tamabayi mama Alhj yace ko zuwa jibi ne ai na kawota dan Habiba sai da lallashi yanzu, babana yace ba komai kasan fushin irin na mai hakuri bai iya ba har na fita babana ni yake kallo bakinshi yaki rufuwa. Goman dare ina kwance kan gadon na murna duk ta cika ni don munyi settling da babana wayata ta soma ruri na duba Adams ne na danyi tsaki sannan na dauka yace yar gidana ya garin?nace yana hannunku yan England to haka ne ni dai na kira ne inji batunmu na runtse ido raina a jagule nace Adam na yarda zan aureka da karfi yace da gaske kikeyi?nace kwarae kuwa,ashe kina sona Maska yace min ba kya sona karo na farko kenan da Maska yayi min karya,na numfasa sannan nace zancen so ai ya kare ko ina sonka ko bana sonka tun da dai nace zan aureka ai shi kenan sannan kayi hakuri Adams ina son barci ne shima sai naji muryarshi tayi sanyi ya bar murnar yace to sai da safe na kiraki kinji?to na gode na tsaya ya kashe wayar sannan na ajiye,daren nayi kuka sosai ba kukan komai nayi ba sai na rasa abin sona shi kenan Adams ne rabona zan auri Adams dan in nuna ma yaynmu cewa tunanin shi ba gasky bane tunda baya sona ne da dai yana sona ne da sai na tabbatar mishi da cewa nima ina sonshi.Washe gari ina zaune akan kujera karama a nan kkfar dakinmu sauran mutanen gida kowa yana yan harkokinsa safa da pant dinsu jamila nake wankewa Sa'a da Bilki suna lido a kofar dakin su mami haj shuwa ce da girki dan haka tana ta kaiwa da komawa,lami mai aiki kuma tana wanke wanke anty mimi ta shigo tayi sallama ban san mai yasa ba duk sanda zanga anty mimi sai gabana ya fadi ita kuma a nata bangaren haka ne abin yake muna hada ido sai ta daure fuska gami da jan tsaki sannan ta kauda kai,su Bilki da Sa'a suka rugo suka rungumeta suna mata sannu da zuwa ta durkusa tana gaida haj shuwa sai ga yaynmu shima yayi sallama daidai sanda na gama shanya pant din ina wanke nawa pantys din,tun shigowarshi idonshi na kaina ni kuma duk da son ganinshi da nakeyi sai naki dubanshi dan ga matarshi kusa da inda nake zaune ya tsaya suna gaisawa da haj shuwa anty mimi kuma ta shiga dakin su mami dan gaida haj kulu,ba kya gaisuwa?ban dubeshi ba nace ina yini?yace ba zan amsa ba tun da ko kallo ban isheki ba bai san duk haushin su nake ji ba shi da matar shi ba,menene wannan kike wankewa a gaban mutane?sai naji kunya duk ta kamani,anty mimi ta fito daga dakknsu mami zata wuce sai yaynmu yace mimi baki gaida maman sagir ba ranta bai so ba haka ta shiga dakinmu data fito yace ta gaida ni na kwanta asibiti tayi jim can tace ya jiki?tayi gaba nima sai nace da sauki shima ya shiga ya gaida mama ya fito lokacin su bilki sunbi anty mimi dakin haj yaya sai haj shuwa a kicin ya dan duka saitin kunnena baa wanke irin wadannan abin a waje sai atoilet kin ji ko?ya wuce na bishi da kallon mamaki na rasa mai yasa yanzu duk ya canza min baya jin nauyin yi min wasu maganganun daidai zai shiga dakin hajyarshi sai ya juyo muna hada ido sai ya kashe min ido daya ya shige dakin na kasa ci gabada wankin dan duk ya saukar min da kasala kamshinshi kawai nake shaka raina yayi fari tas na tattara na koma toilet dana gama kan gadona na haye na dau wayata na kunna dan kasheta nayi saboda ban san Adams na kirana duk sai inji na tsaneshi,text ya shigo min na bude sai naga show message i love you forever na duba. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Yauma kamar kullum zai kai kusan sati biyu kullum sai an min wannan short msg na rasa waye?amma ina ganin Adams ne sai ya wani boye no naja tsaki ya karata nidai ba zan nuna mishi nasan yana yi ba ina yan fadace fadace na sai call ya shigo na duba sai naga yaynmu ne da sauri na dauka hello ki samenj dakin Kabir,hijabi na saka na fito falo mama yaynmu na kirana zai aikeni,to tace min Na fita zaune kan kujera na sameshi da remote a hannu gani na fada ina fubanshi sai naga ya daure fuska dan haka sai nima na shiga taitayina cikin dakewa da miskilanci na shi yace zauna,na zauna ya dubeni da farko ina maki murnar daidaitawa da mahaifinki da fatan ki zama mai mishi biyayya ya cigaba da cewa naji batun Adam's da kuma na gyara papers dinki kin zabga karya kince kina son shi ya harareni ya harareni makaryaciyar banza innaso in miki gata ki samu krt ko da Degree ne ynxu kuma baki son krt ko?nayi shiru ya daka min tsawa bakya jina?bakina na rawa na ce ina son krt mana yace karya ne da kina son krt da kin tsaya kan ra'ayina na sonki yi krt amma sai kika ki kika dauki son aurr kika dora a ranki to muddin kikayi aure ba wani krt da zakiyi lokacin kiyi kuka da kanki ba da ni ba,na dube shi ai Adam's yace zan ci gaba da krtna ya harareni wannan ra'ayin shi ne ina sonki san cewa ba dole bane Adams ya zama mijinki,don ba shi zuciyarki take so ba,haushi ya kamani nace ina sonshi yayanmu ya fusata zan mareki fa,karya na maki kenan?gara ma ki fito ki fadi wa wanda kike so ko zai taimaka miki da sauri na dubeshi yace shiii yi min shiru kin san siyasa na karanta ko?ya cigaba in ina son bararda Adams a wajen su a Alhj a guna abu mai sauki ne sai dai ba halina bane yanzu zan fada miki sirrin zuciyarki,kin kamu da ciwon son wanda kike so tun shekarun baya sai dai baki da tabbacin ko yana sonki dalilin shi ne kika kamu da ciwon zuciya dan kin kasa neman shawara ko mafita kar ki min musu kuma kar kiyi mamaki mutane da dama suna zaton na karanci halayyar dan Adam ne saboda yanda Allah yayi min baiwar saurin fahimtar mutane kin yarda ko har yanzu kina nan kina nan kan cewa ba haka bane?wata zuciyar tace min ki fada mishi gsky wata kuma tace kar ki bada kai,sai nace ni fa ba wanda na taba so ni Adams kawai nake so,ya zuba min ido ranshi in yayi dubu ya bace shi in ban dama yana ganin zubar da girma ne yace yana son yarinyar nan da dai ta yarda da abinda yace to sai ya nuna mata cewa zai taimaka ya aureta dan dai shi ba zai taba cewa yana sonta ba ta raina shi,to ita kuma ga shegen taurin kai ynxu yaya zaiyi kenan?kai shi ai daya san inda ake ajiye so da ya cire inda nata yake ya yar ya huta ya mike tsaye yana dubana sannan yace na zone nayi sallama dake don gobe kamar yanzu muna hanya duk yanda kika ga dama kiyi sai dai zan fada miki wani abu komai ya biyo baya kiyi kuka da kanki zan maimaita miki kiyi kuka da kanki yace kina iya tashi ki tafi sannan in kina bukatar taimako ko na menene kina iya nemana ta waya jikina babu karfi na mike a raina na raya bari na mishi kallon karshe dan haka sai na dube ahi shima ni yake kallo na juya daidai kofar fita na kuma juyowa na dubeshi sannan na fita,gidansu Amira na nufa tana kwance tama aikin karanta littafi kanta na dafaa ina kuka tayi jifa da littafin hannunta ta juyo lfy Iman?me ya faru?cikin kuka nace shi kenan mun rabu tace dawa?nace da yayanmu,sannu kan hankali na zayyane mata komai ta ce kash! Kinyi wauta dakin sani kince mishi kina sonshi menene?ba zan iya ba Amira tunda shifa ba sona ya keyi ba cewa fa yayi wanda nake son zai taimaka min gara na hakura sam ya ma ki nuna cewa shi nake so da kyar Amira ta lallasheni sannan na dawo gida. Kwana biyu duk na rame na fita hayyacina saukin tama naje gidan Babana kamar yanda Alhj yayi alkawari gata dai na duniya ba irin wanda ban gani ba har kasuwa yaje dani can naga yaya Abubkr da yaya Ibrahim don ynxu sun kyaleni,kyauta dai na sameta gurin abokan babana yace yaya Ibrahim ya dawo dani gida ya maida ni Anty Fati sai huci take yi niko ko kallonta banyi ba Anty Maijidda itace matar da babana ya sake aura itama yar cikin kano ce shekara biyu kenan da auran,itama dai shiru ba haihuwa tana da kirki sosai kuma ta nuna tana sona har kitso tayi min dan haka sai nake gurinta,da babana ya dawo kuma sai na koma gurin shi tare muke cin abinci muyi hira ya kan tambaye ni me nafi so ko kuma me na ke so ya sai min?na dinga mishi lissafi ranar da zan dawo sai da muka shiga kasuwa dashi siyayya har ta banza kuma daga kan sutura kayan shafe shafe turarurruka da takalma su Jamila da Sagir kai har su Mami sai da nayi musu tasu tsarabar,Mama da Alhj turare na sai musu sai kace daga wani gari na dawo da ya kawo ni gida kamar kar mu rabu nace zan kuma zuwa ai ya kara bani wata wayar yace shi kadai zai dinga kirana ya samin layin glo ya zuba min no dinshi da ta tsohuwa kakata yace na kira nace zai kawo ni na kwana biyu nace babana na tafi ka gaida Anty Maijidda ta bani tirare tace na ba Mama yace shine baki fadamin ba? nace ita tace kar na fada maka yace to zan mata godiya ki ce ina gaida Habiba har na kai bakin kofa sai yace kin manta da tsarabarki nace lah na mance na dawo ya kwaso min, duk wani motsina idonshi yana kaina kai Babana na sona matukar so.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Kwanaki suna shudewa,Lokaci na kara wucewa mun gama Diploma a Comp, sannan munyi jarabawa sai dai jiran abin da zai biyo baya Adams yana kirana a waya duk da bani sonshi a raina ina dan sauraranshi yaynmu kam bai taba kirana ba sonshi dai yana nan makale a raina ,Alhj da Babana sunyi bincike akan Adams ashe ma mahaifin shi abokin Alhaji Adamu garko ne me gidan Babana dan haka basu sha wata wahala ba wurin bincike sun shirya magana tasu ta manya sannan sunce sai sunji ta bakin Adams sun kira shi sun mishi bayani yayi murna sannan sun bukaci ya fadi daidai lokacin da yake son a sa bikin yace su bashi kwana biyu zai sanar dasu, a son Alhj ayi bikinmu rana daya dasu Mami da Sa'a da Bilki,to amma da kyar hakan zata samu. Yau laraba zaune nake gonar kawu kabiru kanin mama a kauye gefena Jimmala ce kanwar yaya Ibrahim tunda naje kauye kullum sai naje gona kota dangin mama ko ta dangin babana,daga inda nake ina hangen kawuna yana bawa masara ruwa wayata ta soma ringn Adams ne na sani dan haka sai na dauka gami da sallama yar gidana na jima ina nemanki ban same ki ba?nace matsalar ntwk ne yace to ya gari?nace gari na hannunku mutanen England yayi dariya,to yaya?na me? na zancen mu mana kinsan yau ne na yanke musu zan sanar dasu date din daya kamata a sa fa,na dan yatsina baki nace kai yaushe kake so,nafi so asa watan goma kin ga yanzu muna watan hudu nan da wata shida kenan ko?nace to hakan ma yayi daidai, su Mami zasu rigamu dan su saura wata biyu yace insha Allah dani za'ayi bikinsu Mami,Amira fa?nace ita sai tayi HND tukunna yace Ok! to duk yanda sukayi zan kiraki nace kai yaushe zaka zo yace sai bikin su mami zamu zo tare da yaynku ne,gabana ya fadi sam bana son tuna shi dan yaynmu shi kadai nake so so mai tsanani rabona da ganin shi tun bankwanan nan da mukayi yace kina jina?nace ina jinka Adams wai dan Allah kuna shiri da yaynmu?yace sosai ma dashine muka sa date din bikinmu gabana ya fadi nace haba yace Allah gaske ne fa nace suna lfy yace kalau shine ma ya tsaida date don nace nan da four month yace gara six din,nace Allah ya kaimu yace amin... Adams kan abin motsa jiki yaynmu ne ya hada zufa tamkar mai tukin mota yanata faman yi can ya dubi agogon dake manne jikin bangon dakin karfe takwas na safe ya jawo tawul ya soma share gumin da ke zubo mishi sannan yasa baki ya kira Mimi,Mimi ta shigo da sauri gani ya dubeta ina shayin wai yaushe ne zaki koyi yanda ake kula da miji ne?kin san kawo shayin nan aikin ki ne daidai wannan lokacin amma kullum sai nace ki kawo?to za kije ki kawo din koko?kin tsaya min akai,ta juya shi kuma ya ja tsaki sannan ya sauka daga kan abin motsa jikin ya hau kan wata kujera a gefe ya zauna yaci gaba da share zufar,ta shigo rike da kofin tangaran babba da karami,ta ja wani dan tebur ta tura mishi ta juya ba tare da magana ba ya bita da kallo sannan ya girgiza kai sam Mimi bata dace dashi ba ta kowanne fanni sannan yana son a inganta mishi ciki dan kowa ya san yan kwallo da cin abinci,ya kurbi ruwan na lipton mai hade da wasu ganyayyaki can sam sai yaji komai ya ishe shi ya kwana biyu kenan baya cin wani abin kirki tunda Adams yazo mishi da zancen sa ranar shi da Iman ya kuma nemi shawarar sa ya bashi shawara ya bari sai nan da watan goma ne dan yana son ya nemi mafita sam ba zai bari adams ya auri yarinyar da yake masifar so ba,so mai tsanani sannan yasan tana sonshi taurin kaine yasa taki fadi to shima yayi alkawarin sai ya aureta muddin yana numfashi a doron kasa,yayi lissafi Mimi tana da ciki wata biyu zata haihu watan sha daya yana son sai mimi ta haihu sannan ayi bikin nashi ,amma ba zai yiwu ba,ya danyi shiru na wani dan lokaci sannan yace na san abinyi ya mike tsaye ya fita bayi ya shiga a cikin dakin shi ya hada ruwa yayi wanka a gagauce ya shirya cikin JC blue da ratsin fari ya daura takalmi mimi ta shigo kana da bako,ya dubeta wanene?ta dan tsina baki ko Adams yake ne oho?haushi ya kama shi me yasa yarinyar nan batada kunya ne yanxu?amma zaiyi maganainta yace fita anan banza kawai ni zaki cewa baki san Adams ba? ta fita tana yin kuna kunai na gaji da wulakancinka komai kace sai an maka ni ko gsky ko a gidanmu ban kauda tsinke bare wani girki ina dan wanda zan iya kai kuma kana ganin kasa wata yana jiyota sai dai bai san me take fada ba yace zaki gane kuskurenki.Ya sami Adams zaune shima da shiga irin ta Maska Adams ya dubeahi kace ka shirya Maska ya zauna sai dai ban karya ba,haba baka karya ba kai da kake da iyali ma,Maska yace kasan bata da lfy gata dama da son jiki sam bata son aiki Adams yace sai hakuri nidai Allah yasa nayi dace in har ka dace ka sameta din to Adams kar kayi shakka zaka sami yanda kake so,Adams ya ce ya kake cewa in har na sameta?kana ma shakka kenan?kar ka manta fa har na biya sadaki an sa mana rana kuma kaine ma ka tsaida min har na sanar da manya,Maska yayi wani murmushi Adams ya kalleshi Maska bana son wannan murmushin naka fa tuni na sa mashi suna murmushin mugunta dan ko a fili muke gurin wasa abokan wasa suka sako mu a gaba kana irin wannan murmushin sai kaga Allah ya bamu nasara,Maska yace tashi mu tafi a can zan yi break kafin mu shiga fili. Ni kam lokacin ina kauye ranar kwana na sha takwas daga sati daya ina jikin tsohuwa kakata tana fadin daga ni takwara kar ki karasa ni nace kai dan Allah ki barni na dan huta mana infa na tafi sai na dade zan zo tace ai ba zaki kawo min Adamu mu gaisa ba?nace ni ina naga wani Adamu yana can kasashen turawa yana kwallo tace ai Ball yake?ynxu dan Ball din zai rike ki?nace to ai tasu ta gaske ne ba irin ta nan ba,ta tureni ke ja can da ban haushi baga su nan muma muna dasu ba yan bal din yanxu jibi yaron nan na gurin karima shima aikinshi kenan bal asubar fari yasa gajeran wando da wani kwandallelen takalmi raf raf ya tafi bal kusan shekara biyar ance har yau baa taba nuno shi a cikin talabijin ba shi bai tsaya yayi noma ba shi kuma bai tafi rani ba,sai dai yau yana waccan unguwa gobe yana waccan yawon bal,tunda ta soma magana nake dariya,tace dariya ma na baki? dama wannan shirmen Adamun keyi shine za'a bashi mata?ko mu da muke karkara dan gidan karima an hanashi mata,na kuma tuntsurewa da dariya ta dau mafici ta bini kki bani guri ta kai min duka da gudu na fita ina kwasa dariya sai naji tsayuwar mota da sauri na leka motar babana na gani da gudu na fita na taroshi,Ya kira wasu yan samari suka shigo da kayan abinci na rike mishi hannu muka shigo, dakin Baba ya soma shiga kafin ya shiga dakin Tsohuwa na nufi madafi na dauko masa abinci a kwano na debo masa ruwa a randa na aje a gabanshi ina fadin Babana kamar nasan zaka zo na yi abinci da yawa,yace to na gode,nace yasu Mama?yace suna lfy sune ma suka matsa min akan na daukoki daga sati har kin kusa wata jiya Alhj ya kirani a waya yace in mashi kwatance yaje ya daukeki,nadan yatsina fuska nace ni ban son tfy tsohuwa tace to ai ya zama dole nace muna gama bikin su Mami zan taho nan,baba yace a'a muma muna son ki zo mana kafin bikinki daga nan nayi shiru ban sake magana ba,tsohuwa tayi caaraf tace yawwa ashe kai yanzu Adamun dan bal ne?shi ne zaku bashi yar? Babana yayi dariya sannan yace ai sana'a ce sosai suna samun kudi fa shima dan mai gidan Habiba kwallon yake tare ma suke, ai shi kenan amma ko ga tarihi bal ance bata da kyau,yace to ai wasu malaman sunce za'a iya yi in ta zama lalura saboda kishin kasa tace tunda kuna so ai komi ma cewa zakuyi ni dai ina jin su har suka gama. Adamssalin tara text din da aka saba yi min tsawon watanni kullum ba fashi ya shigo,very soon zamu kasance tare domin nasan i am always lucky akan duka abinda nakeso,ban ma gama dubawa ba na kashe yau kamna gane Adams ne yake min text yana boye no haushin shi ya kara kamani na hau fada ina cewa nufin shi sai ya min haka zan so shi?to yayi kuskure ni ba sonshi nakeyi ba zan dai aure shi ne dan hujjar da na ba yaynmu nace kai bari ma in mashi karara don ya daina damuna na soma neman layinshi ai cikin sa'a na sameahi ashe lokacin suna tare da yaynmu a wani club ya dubi yaynmu yace ga yar gidana sannan ya dauka,in kaga yaynmu zaka dauka bai damu da wayar da Adams keyi ba amma ya tattara dukkan hankalinshi gurin sauraron Adams dan ta maganr da Adams keyi zaka gane me nace,ni kam Adams na dauka nace hello Adams menene na boye no kana yi min text in ma kana yi ne dan ka birgeni to wllh haushi ma kake bani,tunda na soma maganar bai tare ni ba sai da nayi shiru,yace calm down my wife wllh ba ni bane ba ban ma taba yi maki text ba nace to wanene?ina zan sani inji adams sannan yace don Allah kiyi hakuri karki damu kanki kashe na kiraki,nace yanzu zanyi shafai da wutiri ne sai da safe yace sai da safen yanda ya amsa har tausayi ya bani,Maska ya dubi Adams dan san jin karin bayani,Adams me Iman tace maka ne?Adams yace wai cewa tayi ina boye no ina kiranta wai bata so Maska yayi murmushi to dama kai kake mata ko?Adams yace bani bane Allah maska yayi tsaki sannan yace kaga abinda nake gaya maku ko ku

Chapter 3 of 5