Share this page
3 / 5
ina sake sanyaya muryata gami da kwantar da kai, sai dai mi, abin da ya futo daga bakinshi ya shafe walwala da farin cikin da ke kan fuskata. "Okay kingama kitsa ganda za ki je ku haɗu da tsohon mijinki ko? shine za ki fake da zuwa duba dangi, dangin da kowa yasan ba ƙaunarki suke ba basu damh da rayuwarkiba, to bari kiji babu ke babu sake taka garinan muddin akwai igiyoyin aurena akanki, ban lamince ki sake yimin magana makamanciyar wannan ba." Yana gama faɗin hakan ya janyeni daga jikinsa ya tashi ya fice abinsa, yayinda ya barni da zafin dukan da maganganunsa suka yi min, da tsananin sauri ƙirjina yahau dokawa, numfashina ya dinga fita da gudu-dugu, nan take shesheƙa ta kamani, idanuwana suka firfito waje tare da sauya launi daga farare tas zuwa jajaye, nan take massarrafar tunanina ta dakata da aiki na tsawon mintuna, ɗiffff haka naji duniyar ta koma min. Kalmar tsohon mijina da ya faɗa itace babban abin da ya rikita lissafina. Fitowa ya yi hannunsa riƙe da key ɗin mashin, da farko bai ko kalli inda nike ba, har yakai bakin ƙofa zai fita, sai kuma ya jiyo cikin ɓacin rai ganin banyi koda motsiba bare ince zan raka shi. Mummunar faɗuwa gabanshi ya yi ganina zaune idanuwa a warwaje inata faman kokowa da numfashina, izuwa yanzu bana iya banbance komi idanuwa sun rufe bana iya ganin komi. "Zainab!!! Zainab!! Zainabbbbb." Ina sam ban san yana yi ba, da sauri ya sunkuce ni yai waje da ni, ko gidan bai rufe ba illa jam luck daya saki ya nufi bakin hanya ya tare ɗan sahu, a gurguje ya faɗa ma shi sunan asibiti mafi kusa du ya rikice, ba zakace Faruk ne wannan miskilin mutumin ba. BAYAN AWANNI HUƊU. Lumshe idanuwa da nike ji sunyinmin nauyi na yi, ga kaina da yake min ciwo kamar zai faɗo ƙasa, akarona barkatai na sake wurga idanuwana zuwa kan wayar Sadauki da ke kawo haske alamar kira, har zan share sai kuma na ɗan muskuta tare da janyo wayar da ɗayan hannuna wanda babu ƙarin ruwa a jiki. Da nasan abin da zaiyi sanadiyar idasa tarwatsa ƴar nutsuwar da na samu zanji, da ko kallon wayar ba zanyi ba, tashin hankalin abin da naji dana ɗauki wayar ya shallake tunanin me tunani, wa ya zazzaƙar murya me kashe jiki na ji ta ce da salon jan hankali. "Hello Sugar, gani na iso tun ɗazu kai kaɗai nike jira kazo ka bani zumarka ko zan samu salama." ban jira ta idasa faɗin abin da zata faɗa ba, na yi saurin katseta cikin rawar murya, dan kunnuwana ba zasu juri jin irin waɗannan maganganun masu nauyi ba. "Me wayar baya kusa." Na faɗa tare da yanke kiran ina bin sunan da aka yi saving number da shi, LUWAI 😋, da alamar emoji me lasar leɓe. Babu abin da yazo kaina sai addu'a nan da nan na cafeta a bakina na dinga jerawa da sauri da sauri, ina jin iska nayimin ƙaranci wajen shaƙa, sai na fizge ƙarin ruwa na sauka daga kan gadon jikina na rawa, ina jin wacce ke kusa da gadona ita da danginta na jeranta min sannu, amma banbi takansu ba na fice ba da sauri. Ɗaga kaina sama nayi ina shaƙar iska me cike da ni'imar Allah, sanyin iskar da sanyin addu'ar da ban daina yi ba na sakamin nutsuwa tare da dawowa cikin hayyacina, nan take wasu zafaffan hawaye suka yiwa fuskata ƙawanya, daga hawayen sai kawai na ɓare bakina na dinga rizgar kuka me ƙarfi, ban damu da yanda mutane ke kallonaba ko kuma masu yimin sanni da kuma masu yimin ta'aziyya a tunaninsu mutuwa akayimin, harma da masu yimin nasiha akan tawassali, rufe idona na yi naci gaba da rusa kukana. Da ɗan gudu-gudun shi ya ƙarasa inda nike, ma'aikacin jinya biye da shi a baya, bai yi wata wata ba ya kaimin wa ta iriyar wawar runguma, sam banyi ƙasa agwuiwaba wajen tureshi da ɗan sauran ƙarfin da ya ragemin, lamarinda ya bashi mamaki matuƙa, ban tsaya anan ba na shiga kakkaɓe jikina inda naji hanninshi ya yaɓa ni, ji nike yi kamar wutace ke ci a inda ya taɓa ni, da runannun idanuwa na watsa ma shi wanni mugun kallo lokacin da ya sake yunƙurowa zai taɓa ni, ban tsaya anan ba na tashi tsaye ina tafiya ina layi bana iya ganin komi sai duhu, a hankali sauti ya ɗauke daga massaragar jina, lokaci ɗaya na yanke jiki na faɗi a sume. Bayan ya tabbatar da ambani kulawa ta musamman, sai ya shiga neman wayarshi amma sai be ganta ba, da farko yayi tunanin ya barota gida, tuna ya ɗaukota kafin lamarin ya faru ya sakashi fara lalube amma wayan, sai roƙar alfarmar wani ma'aikacin jinya yayi ya saka nimbersa ya kira dan aji ko wayar ta faɗi, abin mamaki sai ga ƙarar wayar a kan gadon da nike kwance, da hanzari ya ɗauka tare da yin godiya ga ma'aikacin sannan ya fice waje cikin ujila. Gumi ne ya shiga tsatstsafo mashi yana sharcewa, kokowa ya dinga yi da zuciyarshi da ke gasgata ma shi cewa na buɗe wayar, bama iya buɗewa ba na ɗaga kiran da akayi ƙasa da awa ɗaya. Hannunshi na maƙyarƙyata ya shiga laluben massege app, wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciyace ta kwace ma shi ganin babu saƙo ko ɗaya da aka buɗe. Shanye girman idanuwansa yayi lokacin da ya shiga karanta saƙonin da Luwai ta tura ma shi, sai zuciyarshi ta rabu biyu, ɗaya na ingizashi akan yaje wajenta yaɗan rage zafi tunda dai likita ya tabatar ma shi da babu wa ta damuwa, da zarar ta farka daga barci akaga babu wata matsala za,a iya sallamarsu, sai kawai ya bagarar da zuciyar da ke kwaɓarshi akan hakan, nan take ya tsaida ɗan sahu tare da yi mashi kwatancen inda zai kaishi, kafin ya ƙarasa unguwar Luwai ta kirashi yafi so shurin masaƙi, sai de bai sanar da ita yana hanya ba, sai cewa da yayi ta jirashi zai zo anjima kaɗan. Lokacin da ya ratsa ta cikin gini plaza ya kai ƙarshen shagunan da ke jere reras haggu da dama, sai ya shiga faffaɗan lungunda aka ƙera gida a wajen, gabanshine yaharba da ƙarfi ganin wani tsohon mashin a ƙofar gidan, bai jira komi ba ya isa jikin ƙofar tare da saka makullai ya buɗe ƙofar, cak ya tsaya bai ko motsaba daga inda ya ke tsayen......✍🏻 MARYAM STAR https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133. 💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗 𝘽𝙔 𝙈𝘼𝙍𝙔A𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐ 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪. 𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙊𝙆 BOON ONE 11 & 12-------------Sai da ga gama ƙare musu kallo irrnna takaici da baƙin ciki, harya juya zai fita, sai kuma ya juyo tare da nufaesu gadan-gadan babu alamar sassauci a tare da shi, du yanda Luwai ta so ta kare kanta da faɗin. "Babu abin da ya shiga tsakaninta da saurayin." bai kulata ba saima wasu zafafan maruka daya shiga saukewa saurayin, nan take saurayin yahau ihun yana kururuwar kuka, Sau biyu Luwai na kuskuren kusantar Faruƙ da nifin bashi haƙuri aiko ya sauke mata nata rabon na zafafan maruka, da sauri ta ja da bayan tare da yin zaman dirshan ta shigo sosa kumatukanta da take ji kamar sun daddare saboda azaba. Wasu mutanene su biyu suka zo gibtawa ta wajen plazar sai suka jiyo ihu da farko kamar zasu wuce amma jin ihun na ƙara yawa ya saka suka matsa kusa dan ganin abin da ke faruwa. Da kyar suka janye Faruƙ daga kan saurayin, bayan ya haɗa mashi jini da majina, ba ƙarya ya daku kamar sakwara a turmi. Lokacin da matasanan biyu suka tambayi abin da ke faruwa, Faruk bai san yanda aka yi ba sai ji ya yi bakinshi na furta. "Nasan gidana a kulle ya ke, ban san yanda aka yi waɗanan ƴan iskan suka buɗe har sula shigo su na iskanciba, daga nan police station zan nufa da su, dan bazan yarda ba." Cike da gamsuwa matasan suka yi na'am da zancen Faruk, yayinda ɗaya daga cikinsu ya taimakawa Faruk ta hanyar kiran ƴan sanda a waya, kasancewar akwai ofishinsu kusa, nan suka tsare su Luwai da ke ta fama rusa ihu tana wallahi ba haka aka yi ba, amma babu wanda ya sauraresu da haka har motar ƴan sandan ta ƙaraso, nan take aka kwashesu akai station da su. Sa'ilinda na farka sai na ji jikina sawai babu wannan nauyin, illa kasala data baibaye ilahirin jikina, ban bawa damuwa damar iddabar ruhina ba, dan na rigada na yankewa kaina hukuncin da nike ganin ya dace da rayuwata, fira ce ta ɓarke tsakanina da waɗanda ke kusa da ni, abin da ya yaimaka min sosai na sake samun nutsuwa. Ban kalleshi ba illa sauraren likita kawai da nike yi, ina jin yanda idanuwanshi ke yawo a jikina, nasan hakan bai rasa nasaba sa rashin hijabin da babu a jikina illa ɗan kwalin rigar dana lulluɓe daga kaina zuwa ƙirjina da shi. Har likita ya sallamemu ban ɗaga kaina koda da kuskure na kalleshi ba, lokacin da muka fito wajen asibitinma can gefe na nufa na zauna ina jiran ya tsaida abin hawa, bayan ya gama yiwa me napep ɗin kwatance ban jira cewarshi ba kawai na shige kaina tsaye, abin da ya daskarar da shi tsaye a wajen bai wuce yanda bayan shigata napep ɗin na wuce can bot, nai wa kaina matsuguni, sai da me nafef ɗin ya yi ma shi magana sannan ya shigo ranshi fal mamakin sauyin halina cikin ƴan awanni. Koda muka isa gida ban jera da shi ba, bayan ya gama laluben key ya buɗe, sai yayi tsaye a wajen tare da ƙure ni da idanuwansa da suka sake rinewa zuwa jajaye sosai, kauda kaina gefe na yi, ban nuna alamar na gane mi ya ke nufi ba. Murya a kausashe ya ce da ni. "Zo ki wuce." A maimakon inyi abin da ya ce sai ma sake matsawa baya da na yi, dan ji nayi amon muryarsa kamar yana fita ne da tartsatsin wuta, wutar da Allah ya tanada dan yin hukinci ga mazinata, ni da ban san hawa ba ban san sauka ba tayaya zan yarda ya shafamin bala'i. A fusace ya shige gidan, sai da na tabbatar da ya shiga sannan na bi bayanshi, ban yi gigin shiga ɗakina ba, kaina tsaye na shiga ɗakin da na sauki su Garida, duda babu wani haske, kasancewar ba'a kawo wutar nepa ba, hakan bai hanani lalube na harna samo doguwar rigar abaya da kuma hijabi waɗanda na taɓa ajiyewa Hadiza ƙanwar Faruk da ta taɓa zuwa gidan harta kwana biyu, lokacin da yaronta bayada lafiya. Waje na fita na shiga bayi naɗan watsa ruwa, sannan na ɗaura alwala na koma ɗakin naci gaba da jeranta salloli. Farin ciki wani abu ne da ya daɗe da yin ƙaura daga duniyarsa, kulawa wa ta abace da ta daɗe da yin nisa da nahiyarsa, haka zalika murmushi, zai rantse rabonshi da yin murmushi musamman na farin ciki tun shekarar da ta wuce, wacce ta tafi da duniyarsa gaba ɗaya ta barshi da gangar jiki empty. A yau akuma yanzu da yake tare da Daddy wato mahaifinsa Alhaji Sa'id, ba iya zaman firar da suke yi ba, hadda yanda yake tsokanarshi a cikin tausasan kalamanda ya baibaye massarrafar jinsa da su tun fitowarshi daga gida. Aiki abune da yake yi ba dare ba rana, ya rigada ya saba da yin aiki tuburan, sai de yin aikin kawai yake kamar dole, babu wani nishaɗi a ciki, saɓanin yau, kuma yanzu da yake ta fama aika bayanai a sabuwar computer da Daddy ya gabatar ma sa, badan komi ba sai dan ya dannawar da murmushi akan fuskar ɗanshi, Muneeb mutum ne meson kyauta, koyaya abu yake idan aka yi mashi kyautarshi komi rashin darajarsa, yakanji tsananin daɗi, harma yayi tukuici da abin da ya ninka wanda aka bashi, a yanzunma ɗago da birkitattun idanuwansa da ayanzu suka ɗanyi haske ba kamar ɗazubu, ya watsasu akan Daddy wanda ya kame a kujera yanata rantafo labarai kamar ba Alhaji Sa'id ba, wannan miskilin mutumin marar yawan fara'a da surutu marar amfani. Sai ya zaɓi raba hankalinshi biyu rabi ga aiki rabin kuma ga Daddy wanda ke bashi labarai kala-kala, ciki harda na ƙuruciyarsa wanda koda Mommy baya zama suyi firar amma yau ya zabi bashi labaran, da akazo inda Daddyn yayi tashe rashin ji, musamman jan faɗa da yake yi, har takai idan yaga ana faɗa koda bai san masu faɗanba sai ya siye faɗan ayi da shi, babban abin da ya bawa Muneeb dariya kenan har idonshi ya kawo kwalla, shiko Daddy babu ruwanshi sai rantafo jawabi yake cikin barkwanci. Ranar a office ɗaya suka wuni, su na aiki gami da fira, firarda su dukansu ba zasu ce ga ranar da suka yi makamanciyarta ba, koda kula alokacin baya ne kafin lamurra su ta'azzara. Sai da yamma ta yi liss sannan suka tattare yanasu-yanasu suka yiwa gida tsinke. MARYAM STAR⭐⭐.....✍🏻 https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗 𝘽𝙔 𝙈𝘼𝙍𝙔A𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐ 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪. 𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙊𝙆 BOON ONE 13 & 14---------------Fuskarta ƙayace da fara'a yayinda hasken fuskarta da hasken ƙayatacciyar kwalliyar data caɓa suka sake haskaka murmushinta da wanu yanayi na musaman, yanayinda ya saka zuciyoyin zaratan mazajen biyu yin sanyi da wani abu, wani abu me kama da tsantsar farin ciki gami da alfahari. Wani sanyine ya mamaye zuciyar Daddy, nan take ya ji wani sabon karsashi na ratsa shi, yayinda Mubeen kuma alfaharin kasancewaeta mahaifiya a gareshi ya haskaka zuciya da fuskarshi, atare suka nufe ta fuskokinsu ɗauke da murmushi, itama sai ta shiga takawa cike da ƙasaita zuwa wajensu, a daidai saitin flowers suka tsaya inda sassanyar iska gami da sanyin ruwanda aka bawa flower ya ƙawata yanayin, bata yi wata-wata ba ta fata da kaiwa Daddy sassanyar runguma, shima jira komi ba ya kanainayeta da yashi rungumar kamar zai maida ita cikinsa. Wani abu ne me ƙarfin gaske ya matse gami da dunkulewa waje ɗaya a zuciyar Mubeen. Sake yalwata tashi fuskar yayi da murmushi lokacinda Mom ta janyo nashi hannun shima ta rungumeshi tare da shafa bayanshi sannan ta sake kashesu da kalaman bakinta masu taushi. "Barkanku da dawowa zaratan jatumainahhhhh." a yanda ta sauke kalmar nahhh ɗin sai da Daddy ya matse hannunta dake cikin nashi da dan ƙarfi. "Wash Allah Mom, wallahi har kin kore mana gajiyar da muka kwaso daga yin tozali da ke, gaskiya ke alkairice a garemu Mommy." Ba Muneeb da yayi maganarba hatta Daddy gyaɗa kai kawai ya ke yi alamar tabbayarwa. Haka suka sakata a tsakkiya kowa ya kama hannunta ɗaya suka jera gwanin sha'awa zuwa cikin gidan. "Muƙut" Mommy kubra da ke kallon komi ta saman bene ta haɗiyi wani kakkauran yawu, nan da nan wutar kishi da ɓacin ta ci gaba da balbala a zuciyarta, a fili ta furta. "Na tsaneki baƙar annoba". ta yi maganar tare da kallon saitin Mom dake sakin murmushi cike da nishaɗi, har suka ɓace daga wajen Mom Kubrah bata janye kwayar idonta daga saitin inda suka wuce ba, sai da ta jiyo muryar Meenal a bayanta tana faɗin. "Ki sauƙaƙa wa kanki hakanan Mommy, yawan saƙe-saƙe da tunani bazai amfaneki da komi ba illa cutar da kanki da kike yi ba tare da kin amkare ba, wahalar ta isa hakanan ki fuskanci matsalolinki, ki basu gaba ki tunkaresu kanki tsaye, ko kema kin samu salama da kwanciyar hankali." Wani irin kallo, kallonda ita kanta batasan tana yiwa Meenal shi ba, kawai idonta ya rufe da neman mafita, murya a karye ta ce. "Tayaya hakan zai yuwu alhalin bani da wannan iko da damar, ni ba kowa bace a cikin gidannan, basu ɗaukeni da kima da darajaba, banbancina da ma'aikatan gidannan ƙalilannan, du yanda zan tsara shirina sai ya rushe na rasa ya zanyi, ya zanyi Meenal!!!! ki faɗamin dan Allah." Ta yi maganar hawaye na sulalowa daga kwarmin idonta. "Yanda kika yi a farko haka zakiyi Mommy, dole a sauka ta inda aka hau, kamar yanda na faɗa maki nasan sirrinki, nasan babban sirrin da kike rufewa, sannan kuma nasan abin da ke baki tsoro dangane da lamarin gidanan, idan kina so zan taimaka maki, zai taimake ki kamar yanda kika sakoni cikin plan ɗinki dan kiyi amfani da ni, abu na farko da ya dace ki fara fahimta shine SIRRIN SO💗" Sakato Mommy Kubrah ta yi tana tunani akan maganganun Meenal, wa ta zuciyar na bata shawarar ɗaukar maganar Meenal ɗin wa ta kuma na hanata tare da tariyo ma ta kadan daga hallayar Meenal ɗin. ⭐⭐⭐ Tsawon dare na raya ina nafilfili, koda wasa ban bawa barci damar ɗaukata ba, bawai dan bana jinsa ba, hasalima idanuwa ko buɗuwa basa yi da kyau, na zaɓi ganawa da mahallicina ne akan in kwanta barci, ina buƙatar ganawa da mahallicina dan ragewa kaina nauyin zuciya. WASHE GARI. Da wa ta iriyar azababbiyar yunwa Faruk ya tashi, kasancewa kiya babu kwanciyar hankali sam bai nemi abinci ba, bayan barci yayi nasarar ɗaukarshi can cikin dare ya farka da wa ta iriyar yunwa, sai ya tashi ya shiga dube-dube ko zai samu abin da zai rage hanya da shi amma wayam gidan babu komi, koɗan cincin ɗin da nakanyi in aje babu, hakanan ya sha ruwa ya koma ya kwanta yanata faman juye-juye kasancewarshi mutum marar jimirin yunwa, bayan yayi barci a wahale ya farka, lokacin har jikinshi ya soma rawar mazari, ga cikin shi da ke ƙullewa gami da murɗawa dan azabar yunwa, dakyar ya samu ya lallaɓa kewayen ɗaki ya watsa ruwa, a daddafe yayi sallah sannan ya koma ya zube ƙasa yaraf kamar tsumma. Ganin azabar sai gaba ta ke yi ya samu ahankali ya rarrafa zuwa bakin ƙofar ɗakinsu Ummul inda na kwana, da farko magana ya fara yi can ƙasan maƙoshi, amma daya lura ba jinshi nike yi ba sai ya rarrafa ya shiga cikin ɗaki. A kiɗime na miƙe tsaye ganin mutum ya zube agabana yanata faman maida numfarfashi murya a disashe ya ce da ni. "Zainab ki tallafi rayuwata yunwa zata kashe ni." Tuni na mance da komi na nufi kitchen ina gani dishi-dishi, haka na haɗa gas na ɗaura ruwan zafi, bansaka komi ba illa lipton dana jefa, yana tafasa na ɗauki gwangwanin madara da suger na zuba, na gauraya cikin sauri sannan na ɗauki cup ɗin yana tururi na nufi ɗaki, saboda ruɗewa hakanan da uban zafin na kafa ma shi cup ɗin a baki, bawan Allah hakanan yana ƙone baki da maƙoshi ya shanye shayin tas, da aje cup ɗin bai yi secon biyu ba ya shiga kelaya amai anan wajen, a rikice na dinga jera ma shi sannu idona na kawo kwalla, bai iya amsa ni ba sai kwanciya da yayi a ƙasa yana maida numfashi. Bayan na tattare waje na koma kitchen Indomi na dafa mana guda biyu, dan nima yunwa da barci gaf suke da kaini ƙasa, haka muka cinye taliayar tas sannan muka bi da ruwa, kowa ya koma gefe mukaci gaba da sauke ajiyar zuciya.......✍🏻 M. STAR⭐ https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗 𝘽𝙔 𝙈𝘼𝙍𝙔A𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐ 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪. 𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙊𝙆 BOON ONE 15 & 16--------------------- Haka rayuwa taci gaba da gudana tsakanina da Faruƙ, yayinda na yi matuƙar sauya ma shi, babu wa ta tarairaya da kulawa, abin da ya zama wajibi kawai ni ke yi, ko zama kusa da shi bana son yi, idan ko hannunshi ya kuskura ya taɓa ni, toko ranar wuni zanyi ina goge hannun da wani farin ƙyalle wanda nike jiƙashi da ruwan suratul fatiha, ina gogewa tare da istigifari akan laifin da sam bani da alaƙa da shi. Kafin faruwar wannan abin ina kallon fuskar Faruk da wani irin haske me fitar da annuri na daban, amma yanzu sam bana ganin wannan hasken saima wani duhu me cike da hayaƙi gami da tartsatsin wuta, bawai wuta wannan wacce muke amfani da ita anan duniya ba, wuta irinta azaba wacce Allah ya tanadarwa bayinsa waɗanda sukai butulci agareshi. Kalmar sunan Luwai ta tsaya min ɗas a cikin kaina, kamar yanda nike ji ta tokare maƙogarona ita da wani ƙululu, bawai dan naga sunan a jikin wayar Saraki ba, A,a saboda yanda yake yawan furtamin kalmar alokacin auratayyarmu, nayi ammana da ni yake kira da wannan kalmar idan muna tarawa, ase nayi kuskure wajen amincewa da shi har na bashi duka ragamar rayuwata, a zahiri yana tare da ni amma a baɗini ba ni bace a zuciyarshi, babban abin da ke sake damalmala min lissafi bai wuce yanda zuciyata keson karkata wani waje can daba ba, wani waje ne tsananin nisa da tazara a gareni, wajen da bana tunanin sake takawa, bama wannan ba wajene da na yi tonon rabi na bizne da ƙasa, bayan na binne na bishi da itatuwa na aza akai, sannan na juya baya na barshi, barin da nike iƙirari na har abada, sai de abin da ban saniba shine, kamar na kashe maciji ne amma ba sare kanshi ba, da na sani ban juyo ba na tsaya na fizge zuciyata daga ƙirijina na haɗa da ita a cikin ramin na binne, koyaya matsala ta tunkaro ni a yanzu ko bana son sai zuciyata ta kaini ga tunanin waccan rayuwar, kamar dai yanzu da ina zaune ni kaɗai a gida bayan sallar la'asar, can na jiyo wa ta iriyar hayaniya, na saba jin faɗace-faɗace da hayaniya na tashi a unguwar amma ban taɓa jin irin ta yau ba, a hankali na saka tafukan hannayena akan kunnuwa na danna da ƙarfi, kasancewar bana son hayaniya tun usul, ni macece me gudun wajen da ake hayaniya, dayawan ƙawayena sukan ce da ni, sunan Salaha ya dace asa min saboda sam bana abu da kuzari, komi nawa cikin sanyi nike yinshi, ko magana nike yi a sanyaye nike yinta. Runtse idanuwa na yi ina jin kaina juya min, can cikin kaina wani tunani ya hasko. 🌹Yanayi ne na damuna, bayan angama sheƙa ruwa kamar da bakin ƙwarya, garin ya ɗauki sanyin ni'ima, ko ina yayi fresh, yanayine da ya dace da masoya waɗanda suke cikin shauƙin so, Zaune muku mu biyu rak a cikin rantsetsiyar motar, yayinda fari tas ɗin matashin ke zaune a mazaunin driver, ni kuma ina cure zaune a mazaunin me zaman banza, hawaye ne shaɓe-shaɓe akan fuskata, sai aikin gogesu nike yi amma sam sunƙi tsayawa, du bayan lokaci yakan kalleni sannan ya kauda kanshi gefe yaci gaba da sharara gudu akan shimfiɗaɗliyar kwaltar da ta miƙe samɓal, babu wanda ya ce da ɗan uwansa kanzil a tsakaninmu har muka isa tamfatsetsen gidan, bayan mun shigo ko parking bai gama yi ba na ɓalle murfin da ɗan gudu na fito ina sake fashewa da kuka, bayan shigara falon kaina tsaye na nufi hamshaƙiyar matar da ke zaune akan sofa tana

Chapter 3 of 5