Share this page
2 / 5
Mommy wacce kanta ke niyyar kullewa ta bita tana rarrashi amma a banza ta yi tafiyarta ba tare da ta ko kalleta ba. Sassanyan ruwa ta ɗauko a fredge bayan ta zaunar da shi, da kanta ta kai goran ruwan zuwa bakinshi tare da bisimillah, cikin kukawa da tausasa harshe ta ke yi mashi magana tana shafa hargitsatsiyar baƙa wuluk ɗin sumar kanshi. Ranshi a mugun ɓace ya shigo ɗakin, kai tsaye ya nufi inda suke a zaune ya zauna tare da kama hannayen matashin sannan ya ce cikin ƙoƙarin danne fushinsa. "Muneeb kana ji na ko, please ka nutsu ni da Mommynka muna tare da kai kaji ko". Sai kuma ya janyo ɗan nashi ya rungume cike da tausayi, yana matuƙar tausayawa Mubeen, saboda irin jarabawowi da ƙaddarorin rayuwa da suka yasashi gaba, kullum ahargitse ya ke gwanin tausayi, idan baka sanshi ba zaka iya kiranshi da me maysalar ƙwaƙwalwa, sai de ba haka abin ya ke ba, rayuwarshi ta hargitse ne saboda tarin damuwowi waɗanda suka kasance masu alaƙa da zazzafan so.....✍🏻 𝙄𝙣𝙖 𝙣𝙚𝙢𝙖𝙣 𝙖𝙡𝙛𝙖𝙧𝙣𝙖 𝙙𝙖𝙣 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙙𝙪 𝙬𝙖𝙘𝙘𝙚 𝙩𝙖𝙘𝙞 𝙠𝙖𝙧𝙤 𝙙𝙖 𝙡𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞𝙣𝙖𝙣 𝙠𝙤𝙙𝙖 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙖𝙧𝙖𝙣𝙩𝙖 𝙗𝙖 𝙮𝙖𝙧 𝙪𝙬𝙖 𝙠𝙞 𝙙𝙖𝙪𝙧𝙚 𝙠𝙞 𝙩𝙖𝙮𝙖𝙣𝙞 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 𝙛𝙞𝙨𝙖𝙗𝙞𝙡𝙞𝙡𝙡𝙖𝙝, 𝙣𝙜𝙙🙏🏻 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙎𝙩𝙖𝙧⭐.....✍🏻 Follow the 🌹MARYAM STAR⭐⭐⭐ HAUSA NOVELS AND MORE 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗 𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 & 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮 𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐ 𝙔𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐💪✍🏻 𝙈𝙮 whatsapp 𝙜𝙧𝙤𝙪𝙥 𝙡𝙞𝙣𝙠 https://chat.whatsapp.com/JQlwOnhVAxnFwt1EU6AqU2?mode=gi_t 𝙏𝙞𝙠𝙏𝙤𝙠 𝙖𝙘𝙘𝙤𝙪𝙣𝙩 https://tiktok.com/@maryamumar8361 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* PAID BOOK FREE FAGE BOOK ONE 5&6-------------"Da yardar Allah komi ya kusa zuwa ƙarshe, zaka yi farin ciki, sannan zaka rayu kamar kowa, zaka koma ainahin rayuwarka ta baya, ni da Daddynka zamu kasance atare da kai daga yanzu har zuwa lokacin da zaka samu nutsuwa." Haka iyaye biyu masu tsananin ƙaunar ɗansu suka kasance cikin tattali gami da bawa ɗan su kulawa a tausashe. Cikin raunin murya Muneeb ya ce. " I love you Mom and Dad." yayinda ya ke furta kalmar so ga mahaifanshi, sai da zuciyarshi ta tattare tare da matsewa a cikin ƙirjinshi, yana son yanayin, yana so yanayin ya zamto a tare da shi, sai de kash hakan ba zata faru ba, ya riga da ya sani, faruwar hakan wani abune da baya ganin yuyuwarshi a wannan rayuwar me cike da son kai da yaudara. Iyayen biyu sun kasance atare da ɗansu wanda ke buƙatar kulawarsu, sun yi nasarar fitar da shi daga damuwar da ya shigo da ita, sun wanzar da murmushi akan fuskarshi, sun bashi nutsuwar da ya rasa a safiyar ranar, sannan sun kula da shi kamar ƙaramin yaro. " Kin san wani abu Meenal❓baki da wani amfani sam, babu wani amfani da kika tsinana min illa ɓacin rai da tsantsar tashin hankali, yanzu faɗa min ta ina zan fara gyara wannan aika-aikar da kika yi, tayaya zan tunkari ALHAJI SA'ID CANJI da wannan fuskar tawa, na baki awanni biyu kacal, ki tattara ki koma inda kika futo, bazan ɗauki asara da ɓata lokaci a banza ba saboda shashanci da wauta irin naki." Ido shaye da toka Meenal ta aje tartsetsiyar wayar hannunta sannan ta kalli Mommy cikin ido ta ce. "Humm Mommy kenan, wai ke a tunaninki ke kaɗai kika iya plan, ko kina tunanin ban san abin da nike ba, to tun wuri ki farka daga nannauyan barcin daya ɗauke ki, ni nan Meenal da kikewa kallon shashasha wawuya na fiki sanin takan tsiya wallahi, a tafin hannuna kike domin nasan kaf shirinki na son mallakar dukiyar Muneeb wacce mahaifinshi ya mallaka ma shi, sannan kuma ni da kaina na ce bazan komawa auren Muneeb ba, saboda na gaji da shi, sam banga wani amfani da aurenshi ya tsinanamin ba saima koma baya da asara da na tafka, kina da zaɓi biyu, na farko kodai kisan hanyar da kika bi wajen warware wannan auren a yau ba sai gobe ba, dan na gaji da auren mahaukaci zararre marar amfani, ko kuma ki samamin aiki a CHANJI COMPANY, shima bana so a ɗauki lokaci mai tsayi." Tana gama faɗin hakan ta ɗauki wayarta ta ci gaba da chart. "Ragajab" Mommy ta zauna akan sofar da ke gefen bed ɗin, zufar tashin hankali da kiɗima na gangaro ma ta, a zuciyarta ta ke furta. 'Innalillahi!!!!!, shikenan na gama yawo ni Kubrah, shin ta ina nayi kuskure da har Meenal ta gano babban sirrin da na kwashe shekaru ina ginawa a ɓoye, wait!! shin waima a cikin sirrikan nawa wane da wane ta sani?.' Ta tambayi zuciyarta wacce bata da amsar tambayar. FARUK "Ka yi ƙoƙari ka fara aiki da waɗanan magungunan, sannan kar kayi sanya wajen bin shawarwarin Malam don samun mafita cikin sauƙi." Jinjina kai kawai Faruk ya yi sannan ya ja mashin ɗinshi ya ƙara gaba bayan ya sauke abokin na shi. Baka jin sautin komi sai na ƙarar kiɗan da aka ƙure volume, yaro ne ya shiga gidan sai faman kwaɗa sallama ya ke amma shiru babu amsa, da alama babu wanda ya lura da shigowarshi. Ƴan mata ne su biyu zazzaune ko wace da shigar banza su na ya faman bin waƙar su na jujjuya mazaunai, daga gani ba sai amfaɗa ba kunya ta yi ƙaranci a wajensu, gajiya yaron yayi da sallama hakan ya saka kanshi tsaye ya shiga gidan. "Kai lafiya zaka faɗo mana gida a haka babu neman izini ɗan iskan yaro." ɗaya daga ciki ta faɗi tare da tsaida kiɗan. Ido tsaitsaye yaron ya kalleta gami da cuno baki sannan ya ce. "Wani ne a waje ya ce in kira ma shi Binta luwai." Yaron na gama faɗa ya juya ya tafi yana gunaguni. "Kai wallahi na manta, ashe munyi magana da Faruƙ ya ce min yau zaizo, gashi kuma na shafa'a wallahi." "A hayye cassss, sai da ke Luwai me abin bawa maza, kice yau wannan bakin nawa ya yi shirin cin daɗi, ah maza ki hanzarta shiryawa ki yayo mana rabonmu, ai irinsu Fatuƙ daban suke ba'a yi masu jinkiri." ɗayar ta daɗa fuskarta washe da fara'a. Cikin ƙasa da mintuna biyar wacce aka kira da Luwai ta shirya tsaf cikin ɗamammiyar rigar abaya ta yadin toba, wacce ras ake ganin shatin komi na jikinta, marabarta da tsirara kaɗanne, A hanzarce ta fice tare da yiwa ƴar uwarta bankwana. Ƙanƙame idanuwansa da suka riga suka sauya launi ya yi, tun kafin ta ƙaraso wajenshi ya gama ƙare ma ta kallo tsaf, bai ko jira sun gaisa ba ya tada mashin ɗinsa, hakan alama ce da ke nuna baya son jinkiri, itama bata ɓata lokaci ba wajen ɗannewa kan mashin ɗin, bayan ta gama goga jikinta da nashi. Murginawa yai gefe a gajiye, tare da sauke lumfashi gamsuwa, yayinda zuciyarshi ke sake tabbatar ma shi da lallai Luwai ita ce macen da tasan SIRRIN SO, ita kaɗai ce macen da yake samun gamsashiyar nutsuwa da ita kaf cikin ƴan matan da ya ke bi, yana jinta sosai a zuciyarshi shiyasa baya iya dogon fushi ko gaɗa da ita, hasalima ya saba du sa'adda zai yi tarayya da iyalinsa baya jin cikakkiyar gamsuwa sai ya sake tarawa tare da ita, du yanda ya ke son ya huta hakan bai yuwu ba, a dole ya tashi ta mayyar da kayanshi tare da ajiyewa Binta kuɗaɗe masu ɗan dama sannan ya fice bayan ya aje ma ta key ɗaya daga cikin mukullen gidan. Zaune mu ke muna fira ni da su Farida, inda Ummul ke bani labarin tsohuwar matar yayansu da irin zaman da suka gabatar. "Ai wallahi Anty du haƙurin Anty Yusra kin dameta kin shanye, tana haƙuri da shi amma dai ba kamar ke ba, itafa da wahala a cinye sati ba tare da takai ƙararsa wajen iyayenta ba, tasha yin yaji cikin dare ta tafi gidasu, amma asunar fari mahaifinta ya rakota ɗakinta, shiko yaya ya yi ta ma ta wulaƙanci, gashi tana tsananin son shi, daga ƙarshe dai ƙararshi takai wajen alƙali aka raba auren, bayan ta biyashi sadakinshi dan auren bai wuce watanni tara zuwa goma ba ko Adda." ta yi maganar ta na kallon Farida. "Ih bai wuce hakan ba, amma ai Allah ya saka ma ta tunda bayan rabuwarsu yaya ya gane kuskurensa, kuma yasha zarya wajen ganin ya dawo da ita amma taƙi yarda daga bayama sai jin labarin ta yi aure da yayi, hauka ne kawai bai yi ba alokacin amma sai da ya ɗaga hankalin kowa, sosai na tausaya ma shi a lokacin wallahi musamman yanda ya rasa walwala da nutsuwarshi ya sake komawa miskilin ƙarfi da yaji." "Hummm kuma muncin ubanmu a hannunsa ba, kin manta yanda ya maida mu kamar jakai, baya da aikin sai na dukanmu akan laifi ɗan ƙanƙani, shiyasa nike yin hijira in koma gidan Hajja na kwana biyu." Sosai jikina ya yi sanji, sai na dinga tunano wasu labi'u waɗada nike mamakinsa, a raina na raya tabbas zanci gaba da juriya sannan zan sake dagewa wajen ganin na cike kowace gurbi a rayuwarshi, muna tsaka da firar ya dawo gidan cikin yanayin da na kasa ganewa, duda gabana na yawan faɗuwa idan na ganshi a wannan yanayin ina daurewa sosai wajen ganin na hana zuciyata yin tunani sai de kuma wani lokacin tsoro na sake baibayeni idan na nutsu sosai ina nazarinshi. Kwanci tashi asarar mai rai, har anyi biki angama su Farida sun koma gida, ambarni daga ni sai Sarakina wanda izuwa yanzu mun cika wattani takwas da mallalar junanmu, sosai na dage wajen ganin na zama tauraruwa me haske a rayuwarshi, na ƙara ƙaimi sosai wajen kulawa da shi, sai de a hankali ya ke sauya min, ya rage bani lokacinsa sannan yanzu na fuskanci yana yawan yin waya, bayada haka yanzu yana yo dare sosai a waje, kuma baya bani fuskar da zan yi ma shi magana akan haka, dayake ina ɗaukar abubuwa da sauƙi sai na ɗaura alhakin sauyawarshi akan yawan hidima da zirga-zirgar kammala aikin plaza da aka yi, a halin yanzu ana shirin buɗeta ne dan har ansaka rana da lokaci. Idan aka cire bauɗaɗun hallayar Saraki, bani da wa ta matsala, hankalina a kwance ya ke, na samu yanda nike so, shiyasa na fara tunanin kai ziyara wajen ƴan uwa da dangina, dangin da abaya ko ƙaunar tunaninsu bana yi, saboda izaya da baƙar wahalar da nasha a wajensu, yanzu kam na samu tsuwar tunkararsu kaina tsaye, tun da yanzu ikona ba ahanunsu ya ke ba.....✍🏻 Please share fisabilillah🤌🏻🙏🏻. NI CE TAKU MARYAM STAR⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU💪 https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m13 💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗 𝘽𝙔 𝙈𝘼𝙍𝙔𝙒𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐ 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪. 𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙊𝙆 7&8------------ Cikin taku me cike da nutsuwa ta ke takowa zuwa gareshi, yayinda hani haske me kaifi ke zagaye da ita, a daidai saitin inda ya ke durƙushe dafe da kai ta tsaya tare da sakar ma shi wani sassanyan murmushi me kassara nutsuwar gangar jiki, ɗaga siririn hannunta me fitar da haske ta yi tare da miƙa ma shi alamar ya kama, da hanzari ya tashi tare da miƙa ma ta hannun na shi, sai de hannayensu basu kaida haɗuwa da junana wa ta ƙaƙƙarfar igiya ta wanzu a tsakani, nan ta ja wannan macen me tsananin gaske zuwa baya, duda igiyar na janta hakan bai hanata miƙo ma shi hanunta ba fuskarta ƙayace da murmushi, da hanzari ya miƙe tsaye da tsananin gudu yana son cin ma ta, amma ina tuni haskenta ya disashe nan take ta ɓace ɓat daga ganinshi, wa ta murya ya ji daga sama na faɗin. "Sirrin so kenan, ita ce sirrin son ka, zata dawo gareka da farin ciki marar yankewa, sai de kuma kafin haɗuwarka da ita dole ne sai ka...." Da wani irin sauri ya muɓe idonuwanshi da suka yi jah sosai, bai sauke su ako ina ba sai akan fuskar mahaifanshi biyu, inda ya gansu tallabe da shi sai faman sauke ajiyar zuciya suke a jajjere. "Son kana lafiya❓." Mom ta yi maganar fuskarta ɗauke da damuwa. Sake buɗe jajayen idanuwanshi ya yi tare da watsasu akanta cikin murya ƙasa-ƙasa ya ce. "Ita ce ta sake zuwa, anfaɗa min ita ce sirrin so, zata bani farin ciki, ita ce makullin buɗe ƙofofin farin cikina Mommy, please ya za'ayi in sadu da ita." ya yi maganar kwalla na gangarowa daga idanuwanshi. "Ba tun yauba nasha faɗa maka, ba lallai mafarki ya kasance gaskiyaba, zamu kasance masu tayaka da addu'a in sha Allah komi zai koma normal, zaka yi rayuwa kamar kowa, sannan zaka yi farin ciki kamar baya, muna tare da kai." Mommy ta faɗa a daidai lokacin da ta zame hannayenta daga ruƙon da ta yi ma shi. "Muje ɗakina ka watsa ruwa sai mu wuce office tare." Daddy wanda jikinshi ya yi sanyi ƙalau da yanayin Muneeb ya faɗi tare da miƙewa, miƙewa tsaye Munneb ya yi tare da bin bayan Daddy suka fice. A gurguje ya yo wanka tare da shiryawa cikin manyan kayan da Daddy ya aje ma shi, dakakkiyar fara ƙal ɗin shadda ce ɗinkin zamani, sai ƙyalli gami ɗaukar ido ta ke na sabunta, Daddy na murmushi ya matsa kusa da shi tare da kafa ma shi hular da ya aje bai saka ba, yah Rahaman, kuzo kuga kyau, kwarjini gami da kamala da suka yi ƙawanya akan fuskar Muneeb, ba zaka kuce shine wanda ya shigo gidan ahargitse kamar mahaukaci ba. Murmushi Muneeb ya saki kamar yanda Daddyn shima ya yi, sannan suka saƙala hannayensu cikin na juna suka fara takawa kamar masu abokai, yayinda hannun Muneeb ya shiga cikin na mahaifinsa, nan take wa ta nutsuwa ta baibaye ilahirin sassan jikinsa da ruhin sa, yakan ji cikakkiyar nutsuwa idan yana tare da iyayensa masu ƙaunarsa. "Akwai babbar matsala Suhama, waccan yarinyar da nike yiwa kallon shashasha ashe tasan komi, kar ta ke kallona, hasalima nice babbar shashasha da nike ƙoƙarin turata inda zata hallaka ni, please kiji da wannan lamarin ni kuma zanyi ƙoƙarin kashe wutar da ke neman ruruwa a gidannan, muddin Alhaji Sa'id ya saka ƙafarsa ya fice a gidannan ba tare da munyi magana ba kashina ya bushe, samun kanshi zai yi min wasala a yanzu, dama aɗofane ni ke wallahi, kiyi abin da ya dace sai munyi magana." Mommy ta yi maganar tare sharce zufar tashin hankali da ke tsatstsafo ma ta, a hargitse ta ajiye wayar tare da ficewa daga ɗakin. Mummunar dokawa ƙirjinta ya yi ganin taurari biyu masu tsananin haske na tafiya hannayensu sarƙafe dana juna, ga wani annuri da ke fita daga fuskokinsu, kamar sakarai haka ta wani saki baki da hanci tana kallonsu, bata san sadda suka ƙaraso gabanta sai gani ta yi sun giftata sun fice suka barta da ƙamshim daddaɗan turarenta, sa'adda ta dawo hayyacinta tuni sunyi ma ta nisa, domin har sun fice daga gidan cikin tsadaddiyar motar Daddy, sai gani ta yi Sojan me ganin gidan na ƙoƙarin rufe get, gudu-gudu sauri-sauri haka ta fice tare da faɗin. "Tsayar da su Bola, tsaida su sunyi mantuwa." amma ina sam bai jitaba saboda tazarar tafiyar da ke tsakanin get ɗin da inda ta ke, cike da takaici ta juya zuciyarta na luguden duka, ga tashin hankalin abin da idanuwanta suka gane ma ta, sai abin ya haɗe ma ta goma da ashirin, cikin rasa abin yi ta zube "jagwab" akan sofa tare da maida numfashi. "Mamy ba za ki gane ba, wallahi du wayanki wannan matar ta dameki ta shanye, kuma nidai gaskiya ba zan iya wannan aikin ba, dolene yau ba sai gobe ba arabani da wannan alaƙaƙƙaiɗin jarababben auren wanda banga wa ta riba tattare da shi ba." cewar Meenal muryata can ƙasa-ƙasa da alama bata son aji wayar da ta ke. "Kull Meenal kar in sake jin wannan maganar daga bakinki, dolene ki tsaya kiyi yaƙi domin ki inganta gobenki, so kike yi ki zamo kamar ni ɗinan ban aje ba ban bawa wani ajiya ba, ki kwantar da hankalinki kinji ƴa ta, dukiyar Alhaji Sa'id kina da haƙƙi a cikinta, kuma ya zama dole kema ki tsaya tsayin daka ki kwashi naki rabon, tun kafin wannan baƙar muguwar ƴar uwar tawa wacce kanta kaɗai ta sa ni, ta yi bake-bake akan komi, ki sauraurare ni zuwa anjima zamu idasa maganar, amma maganar tahowa London ba mafita ba ce, dole ki tsaya kiyi yaƙi akan gobenki kin ji ƴata." Muryar wacce aka kira da Mamy ta faɗa daga can cikin wayar, a taƙaice suka yi bankwana da junansu suka datse kiran. Zama Meenal ta yi tare da tunano abin da ya faru safiyar yau ita da Muneeb. Kwance ya ke akan lallausan gadonshi yana barci, da alama bai yi shirin yin barcin ba, dan ƙafafuwanshi sanye suke cikin takalmi have cover, sannan kuma dokayen ƙafafuwan na shi basu idasa hawa gadon da kyau ba. A hargitse ta shiga ɗakin na shi, tare da watsa idanuwanta akanshi, sam babu cikakkiyar nutsuwa tattare da ita haka ta ƙarasa inda ya ke kwance, ba ta jira komi ba ta shiga ƙoƙarin tashinsa daga barci, bata yi la'akari da yanayin da ya ke barcin ba, ita dai burinta kawai buƙatarta ta biya. Can cikin barci ya fara jin abin da ta ke yi ma shi, a hankali ya shiga buɗe birkitattun idanuwanshi, kai tsaye ya watsa su akanta, a ɗan fusace ya miƙe zaune yana jin yanda kanshi ke sarawa, tun kafin ya daidaita zamanshi ta faɗa jikinshi tare da yi mashi abin da sam baya da buƙata a lokacin, shiru ya yi bai kulata ba saima gyawa zamanshi da yayi tare da zuba ma ta ido yaga gudun ruwanta, du ƙoƙarinta na ganin ta cimma nasara abin ya gagara hakan ya saka ta ɗaga idonta a birkice tare da gaya ma shi maganar da ta saka ya wanke fuskarta da zazzafan mari, bai tsaya anan ba sai da ya zanyeta daga kan gadon a dusace. "Sakaran namiji kawai marar amfani, wanda bai iya komi ba sai baƙin hali da hauka." Ta faɗi cikin jin zafin abin da yayi ma ta. Sosai kalamanta suka sokeshi, amma sai bai kulata ba ya koma ya kwanta yanajin kanshi na sarawa sosai, ga wa ta irin gajiya da ke sauko ma shi sanadiyar kwana aiki da yayi, babu abin da ya je buƙata sama da hutu....✍🏻 Idan kunji daɗin wannan page ɗin kuyi like, comment, and share domin ƙarfafa min gwuiwa. NI CE TAKU MARYAM STAR⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU 💪 https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m13 Follow the 🌹MARYAM STAR⭐⭐⭐ HAUSA NOVELS AND MORE 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel /0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 💗𝙎𝙄𝙍𝙍𝙄𝙉 𝙎𝙊💗 𝘽𝙔 𝙈𝘼𝙍𝙔A𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐ 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪. 𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙊𝙆 BOON ONE 9&10 Nan da nan jikinshi ya ɗauki rawar macin rai, yana takaicin yanda Meenal ta ke sakin magangani babi tsari kamar ba mace ba, ga rashin kunya da fitsara, idan ya zauna ya zurfafa tunani akanta sai ya rasa dalilinshi na aurenta, sam bata yi kala da macen da ya ke so ba, yana kaiwa nan a tunaninshi ya sake jiyo sautinti ta na faɗin. "Yo ba dole baiwar Allar da aka ƙaƙaba ma ta kai ba ta gujeka, wannan irin baƙin hali da tauye haƙƙi, ai wallahi tayi min daidai data rabu da kai, baka da wani banbanci da mace, garama wa ta macen da kaiii....." Ta aje sautin cikin kururuwar ihi saboda zazzafan marin da ya sauke ma ta, wasu fararen taurari ta gani su na shawagi a masarrafar ganinta, kafin ta dawo daidai ya ɗora da faɗi a zafafe. "Ke wace irin yarinya ce marar hankali da tunani, wace irin kwanya ce cikin kanki da sam baki da ganewa, wallahi badan kar in sake yin kuskure akan kuskure ba, da babu abin da zai hana in datse alaƙa da ke." Ya yi maganar ɓacin rai na bayyana a murya da kuma fuskarshi, a fusace ya fita zuwa parking lot ya shiga mota da niyyar barin gidan, sai de yana fita itama ta fito hannunta riƙe da key ta ɗauki tata motar tabi bayanshi. Haka suka dinga tseren gudu a tsakaninsu shi yana gaba ita tana biye da shi a baya har suka isa family house. ⭐⭐⭐ "Na shiga uku ni Meenal shikenan na idasa ruguje komi, wai miyasa banyi tunani ba kafin in aikata abin da na aika, oh mah god ka taimake ni." ta yi maganar tana cizon yatsa, can ta miƙe zunbur kamar wacce aka mintsina ta yi hanyar main falon cikin sanyin jiki. Mom ce zaune akan dinning tana karyawa da zazzafar nodles da ta saka aka dafa ma ta, dan bata samu ta karya ba a ɗazu, tana ganin yanda Meenal ta taho jiki a sake amma ta share ta yi kamar bata ganta ba. "Mom, barka da yau." Meenal ta faɗa tana sake shan jinin jikinta ganin yanda Mom ta haɗe sama da ƙasa, sau ɗaya Mom ta kalleta ta watsar ba tare da ta amsa gaisuwar ba. Wash ƴan guntun hawaye ta ƙaƙalo sannan ta ce. "Please Mom for give me, wallahi mistake aka samu, amma i promise you hakan ba zai sake faruwa ba in sha Allah." Nisawa Mom ta yi sannan ta ce. "Uhumm Allah ya yarda." Du wanda Meenal ta so Mom ta saki jiki da ita abin yaci tura, da ace tana da lura da tuni ta gane Mom ɗin bata ita take ba, abincinta ta ke ci tare da latsa dalleliyar wayarta, jifa-jifa takan saki murmushi, saboda sakarci sai Meenal tayi tunanin Mom ɗin ta sauko, da Mom ta gama abin da ta ke ta umarci masu aiki da su kwashe komi na wajen, ita kuma ta tashi cikin ƙasaita gami da izzar kuɗi ta wuce ɗakinta, sai ga Meenal zagaram-zagaram ta bi bayanta, Mom bata lura da ita ba sai da ta isa jikin ƙofar daƙinta wacce ta kasance ta glass, sai ta hangi mutum a bayanta, aɗan fusace ya waigo tare da watsa ma ta kallon lafiya, ɗan daburcewa Meenal ta yi tare da faɗin. "Am,, umm,,, dama,,,, dama ina so zan tayaki zama ne kafin su Honey su dawo daga office." Kallon baki da wayo Mom ta jefeta da shi, kafin a miskilance ta ce. "Ba buƙata." ta dannan madannan password na ƙofarta ta shige tare da saka lock. A sanyaye Meenal ta juya tana jin du ta muzanta da abin da Mom ɗin ta yi ma ta, tayi mamaki sosai da hakan dan zata iya rantsewa da Allah Mom ɗin na tsananin kulawa da ita, idan ta zo gidan ta dinga nan nan da ita kenan cike da kulawa, amma yanzu ta wani ɗibeta ta watsar. 🌹🌹🌹🌹 Kwance nike akan fafaɗan ƙirjinshi, yayinda nike ta kokowa da maganar da nike son faɗin tun ɗazu, da kyar da daure na ce cikin sanyin murya. "Am, Saraki kaga yanzu da yin aurenmu an kwashi watanni, kuma tun bayan da na tare a gidannan ban sake taka ƙafata garin ba, wallahi nayi matuƙar kewarsu, dan Allah kabarni inje inga dangi da ƴan uwana." na yi maganar

Chapter 2 of 5