Share this page
6 / 7
tace ke bani son rashin kunya Amira tace ba rashin kunya bane ance ne mu juya dashi na dubi Amira nace don Allah ki rufa mani asiri Amira ta jani zamu juya Anty mimi ta biyomu ta fisge jakar ta juya ni dariya ma abin ya bani,muna jiran mai mashin wani yazo da mota a gabanmu ya tsaya ya dube mu yace kuzo muje yanmata ina za'a kaiku?kafin nayi magana Amira tace unguwar rimi na dubi Amira nace kina hauka ne?tace zauna nan in ba zaki ba sai dai kiyi ta zama anan yace magana fa nakeyi nace ku shigo muje nima can na nufa,nace nidai ba zan shiga wannan motar ba Amira ta bude baya ta shige sannan tace ai kina da kudin mashin ko?nan na tuna bani da ko sisi nayi tsaki,saurayi mai mota yace yar kanwata shigo mana jan ajinki ya burgeni kuma na yaba,na dubi Amira ta wani kame tamkar motar kanin babanta nace bani naira dari tace nace maki bani da kudi ko?in zaki shiga ki shigo dole,dole na shiga motar nima bayan na shiga yace yi hakuri kanwata dan dawo nan mana na koma don surutun ya soma isata yaja muka tafi,sannu a hankali yake jan motar sunana ya tambaya nace mashi Amira, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Amira da take baya ashe taji tace yar iska sunanta Iman yace yauwa mai sona fada min gsky Amira ta cigaba da cewa xan kaika har gidansu yanda tace maka haka takeyi ma samari tace sunanta Amira kuma ta yi masu kwatancen gidanmu ina jinsu ban kuma magana ba sai su keta faman labarinsu,muna zuwa kofar gidanmu ya faka a daidai lokacin yayanmu yayo ma abokanshi rakiya kallon motar ya tsaya yi da sauri na bude na fito daga motar ido hudu mukayi da yayanmu nan da nan fuskarshi ta sauya yayi murtuk tamkar bai taba dariya ba koda dai dama ban taba ganin dariyar tashi ba,a hankali yake tahowa har inda muke nayi zaton zai mare ni ne sai naga ya wuce ya isa gun motar daidai kofar dreba ya kwankasa gilashin motar,ina zaton Amira da bata fito ba ita ce tace masa yayanmu ne sai naga ya fito daga cikin motar da sauri sannan ya mikawa yayanmu hannu gami da sallama,yayanmu nokewa yayi yaki bashi hannu sai dai ya amsa sallamr a ciki ya dubeni yace menene dalilinki na shiga motarshi?nayi shiru shi kuma saurayin mai motar sai cewa yayi yallabai ai ina sonta ne kuma banzo da wasa ba,sai ya kara daure fuska sannan yace ita me tace maka?yace bamu yi magana ba tukunna,yayanmu yayi mishi wani kallon wulaknci sannan yace kar na kuma ganinka a gidan nan ka fahimceni? yarinyar nan krt zatayi ku ne masu hure ma yaran mutane kunne suki krt bani bukatar sake ganinka understand?so kama gabanka ya juyo ya kalleni wata uwar harara ya sakar mani ba zaki wuce a nan ba? Da gudu nayi cikin gida. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Tara daidai na dare na gama shirin kwanciya kamal ya shigo ya dubeni ke Iman yayanmu yace kikai mashi tea,ban tsaya dogon turanci ba na fito falo dakin mama na shiga ko zan samu ta dafa ma Alhj bata cikin dakin na fito falo kan tebir naga ples din shayi na duba naga akwai a ciki yar butar shayi na dauka na zuba na dora kan tiranshi na hada da kofunan na fita sam na manta ban sanya hijabi ba rigar bacci ne a jikina mai hawa biyu sai hular hijabi nayi sallama da kyar ya amsa na dan dube ahi fuskarshi a daure cikin tsoro na shiga zaune yake kan kujera mai zaman mutum biyu ya dora kafarshi suna kan teburin tsakar dakin irin dan karamin nan na rage tsahona na ce gashi ya zuba min harara na ajiye da sauri na zan fita sai naji yace ke zo nan na daqo ya dubeni yace zauna na zauna kan kafet cikin hankali ya sauke kafafuna daga kan tebur din ya zauna da kyau,Amina naji ya kira sunana a hankali yar naji cikin jikina gashi ya iya fadar sunan a gajiye na dubeshi sannan na amsa yace na lura dake kina shaawar ganin bacin raina ko? (hhahhh su yaynmu anyi nisa) na girgiza kai alamar aa yace haka ne mana(a raina nace to me nayi maka?) Yaci gaba in ba haka ba so nawa zance miki bani son kina kula samari ko kema auren kike so?nace aah yace kar ki damu in ma auran kike so to sanar dani don akwai wani da yayi mani maganar yana sonki,gabana yayi mugun faduwa a raina nace ni kai nake so ya kara tausasa murya yace in har kina so ya kara tausasa murya yace in har kina so ki kwantar min da hankali to ki tsaya kiyi karatunki kar ki damu da su mami basu san matsalolin da ke cikin auran ba,kinga kema karamar yarinya ce baki san komai game da aure ba undaerstand me?na gyada kai alamar eh yace to yi min alkawari da bakinki cewa ba zaki kula kowanne da namiji ba ko bana garin ko bana kasar har sai na dawo na bada izini ba tare da wani tunani ba nace nayi alkawari ba zan kula kowa ba ko ba kanan yace promise nima nace promise yace good ya saki fuska tashi kije ki kwanta na mike sai da naje kofar fita na juyo shima ni yaje kallo ga mamakina sai naga ya min murmushi mai tsayawa a rai na saki labulen na tafi zuciyata na dauke da murmushin da yayi min,haka na kwanta ina juya maganganun da yayi min musamman in da yake cewa in har kina so ki kwantar min da hankali to ki daina sauraron samari me yake nufi?wata zuciyar tace min abokinshi mana haka nayi ta juyi har barci ya daukeni Washegari da safe ina shirin tfy comp Jamila da Sagir suka shigo da gudu suna rige rigen fada min kiran yaya Kabir na daka musu tsawa nace kai ba makaranta zaku je ba?suka ce ai mun fita sai yayanmu yace kizo nace yayanmu babba?suka ce a'a Kabir,na dan yi tsaki sannan nace kuce gani nan,sagir yace anty kizo muje yace in kika zo muje yace in kinzo zai bamu naira 100 nace ku bace min da gani a nan suka fita sai da na gama sannan nayi wa mama salla.a sannan na fita,na dauka ya tafi gun aikinshi sai na ganshi a kofar dakinshi sai faman duban agogo yake yi na isa gurin shi fuskata babu walwala nace ina kwana?bai amsa ba sai dubana yake yana murmushi yace da raina ya baci domin kin shanya ni amma yanzu kin wanke min zuciyata na dubeshi nace kamar yaya?kinyi dressing irin nawa,na dubi kayan jikinshi kampala green nima haka sai naji tamkar na koma na cire ya dube ni zo muje na saukeki nace ka barshi yace duk da nayi latti sai na kaiki,dole na shiga muna shirin fita yayanmu ya shigo shi da wasu abokanshi cikin kayan training duk da kaninshi ne sai da gabana ya fadi yako tsira mana ido sai ya tsaida motar ya dubeni yace kin mani shara?na dubeshi yayi wani kicin kicin nace a'a yace to fita ki min bai saurari amsata ba yayi gaba na dubi yaya Kabir nace to kaji fa abinda yace,yaya Kabir yace don Allah ki rabu dashi bari mu tafi,nace wai ba haka a tsakaninmu haushi ya kama yaya Kabir yace toko dai yana sonki ne?nace kaji ka da wata magana kaima kasan ko mata sun kare yayanmu ba zai soni ba yace saboda me kikace haka?nace ni nasan bani da kyau kuma gani baka yayi murmushi sannan yace ganinki kenan kina abubuwa masu fizgar hankali so ni dai yanzun ki yarda na fito sai a hada da nasu Mami,haushi yasa na bude motar na fito shima yayanmu na sameshi ya cika dam ina shiga ya dube ni duban wulakanci yace me kika tsaya yi a gunshi?nace ba komai ya nuna ni yace look ba zaki min yawo da hankali ba bani son na kara ganin kin shiga motar Kabir kina jina?ya daka min tsawa nace to,ya fita na shiga gyaran daki ina mamakin wannan ikon Allah.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Ina cikin goge TV ya shigo yana waya ya zauna kan kujera yanda naji yana amsa wayar ne yasa naji duk bakin ciki ya kamani ko bai fada ba nasan da Mimi yake magana har yana cewa karki damu nima kin manne cikin raina kuma ki saurareni in anjima da sauri na shiga bedroom dinshi har lokacin wayar yakeyi ranar da takaici na yini wata zuciyar tace min kina kishin banza kina wahala bai san ma kinayi ba Kwana biyu ni dasu yaya Abubkr da duk wani mai son ganina in dai saurayi ne sai dai a waya ranar juma'a ina zaune da yamma tsautsayin jin takaici ne yasa nace da mama bari in shiga gun Amira ina isa daidai dakin yayanmu shi kuma yana fitowa tare da abokinshi sun kai su bakwai daya ne naji yana cewa ango ango to Maska wata nawa aka sa yayanmu ne naji ya amsa da cewa sati biyu suka sa da sauri na juyo cikin sa'a muka hada ido shima sai naga yayi wani iri tamkar bai so naji zancan ba wani abu mai nauyi naji ya tokare min wuyana kirjina kuma ya hau zugi da kyar nake janyo numfashina kokari nayi naci gaba da tfy amma bana ganin gabana sosai jirin da naji ya soma dibana shi yasa na juyo na koma gida ikon Allah nema ya kaini kofar dakinmu a nan na zube ban kuma sanin in da kaina yake ba na dai farfado na gani a gadon asibiti Mama tana zaune a kan kujera tana rike da hannu na wanda aka sa min karin ruwa ta min sannu na amsa da kyar a hankali na soma tuno abubuwan da suka faru shi kenan yayanmu ya zama na Anty Mimi ko shakka babu yana mutuwar sonta,na tuno wata rana ina shara a dakin yaynmu har na gama zan fita yace nazo nan na juya na koma nace gani yace baki sa turaren daki ba nace na mance ne,na shiga bedroom din shi idona ya sauka akan wani kyakyawan frame kamar kaida in dai zan shiga uwardakin yayanmu to ba abinda nake fara kallo sai wannan frame din yana da kyau ga dauakar hankali gashi saitin kofa da ka shigo shi zaka fara gani,na manta batun turaren daki na tsaya duban frame rubutun jiki yan kanana shi yasa ban taba karantawa ba amma lokacin sai na hangi rubutun saman kamar hausa akayi nayi mamaki frame mai kyau da shegiyar tsada irin wannan amma da hausa na ce kai yau sai na dauko shi na karanta duk da wane yare ne na duba dakin ko naga abinda zan taka don yayi sama sosai ba wani abu mai tsawo sai tebur karami kuma na glass ne na jawo shi a hankali na taka daya ke nima ina da tsawo na dauko,tabbas da hausa akayi rubutun a saman an rubuta: Zinariyata Zuciyata ta jima tana begenta daga lokacin da idanuna suka fara ganinta,na tsunduma a sonta duk karancin shekarunta duk sanda na dubi idanunta sanyi kasala sha'awa suna gajiyar dani bare in naji kamshinta,a lokacin da nayi nisa da ganinta sai barci ya kaurace ma idanuna sai tunaninta bana jin dadin wani girki sai nata Allah ka azurtani da aurenta domin na samu ni'imarta har ka azurtani da 'ya'ya masu albarka daga gareta (A)amin. jikina yayi sanyi sai dai abin daya bani mamaki shine yanda (A)a cikin (A)tamkar irin na zoben da yayanmu ya bani a cikin kayan tsaraba nace kai kilan ma ba (A)guda biyu ba ne wani tambarin ne na wani camfanin a can England din,na dubi fulawoyin dake jikin frame din da tsuntsaye masu ban sha'awa ina cikin juya shi ina cewa nasan Mimi yake nufi,shine Mami tace min baya sonta ashe ma ya jima yana sonta gashi yace tun tana karama,ina cikin tunani naji yayanmu daga falo yace baki ga turaran bane?nan jikina ya soma rawa ina kokarin maida wa ne tsautsayi yasa na goce,frame din ya fado sai kan tebur din glass ji kake tats,jikina ya hau bari na soma tsuma tamkar mazari,na dauki frame din baiyi komai ba teburin ne ya fashe naga an daga labule da sauri na dubi kofar yayanmu ne tsaye nayi duba zuwa ga fuskarshi ya wani daure fuska me ya kai ki gurin frame kina ganin sirrina ko?hawaye ya soma zarya a kan kumatuna nace a'a zan goge ne yayi kura ya daka mani tsawa yi min shiru kuma sai kin biya dukkan abinda kika fasa min,na durkusa kan gwiwoyina na soma cewa don Allah kayi hakuri yace ai zaneki zanyi yanzun nan muryata tana rawa nace please yayanmu ya dubeni cikin wani yanayi mai wuyar fahimta sannan yace gyara min wirin ki wuce,ban san kan kwalba nasa gwiwata ba sai da na gama gyra dakin sannan naji zafi na duba.kamshin turaren da naji shi ya dawo dani cikin hayyacina ko ba'a fada ba nasan yayanmu ne ya shigo Asibitin nan ban gama tunani ba ya kwankwasa kofa ya shigo dama fuska ta kofa take kallo don haka yana shigo dani muka soma hada ido sai naga tamkar an kara mashi wani kyau.... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Na lumshe ido sai naji wasu hawaye sun zubo min ina jinshi suna gaisawa da mama ya tambayeta jikina tace da sauki ban ma san har na kwana ba sai da naji yace tun jiya bata tashi ba?mama tace dazun nan ta farka ina mata magana banji ta amsa ba nayi mata sannu ta amsa bata kuma magana ba sai hawaye da ke zuba daga idonta shiru yayi na dan lokaci sannan yace bari inga likitan mama tace yanzun nan babanku ya tafi gurinshi tun jiya ma yace ciwon zuciya ne yake son kamata ni na rasa mai yarinyar nan ta nema ta rasa da har ta sa kanta cikin tunani,muryar yayanmu naji cikin sanyin shin nan yace ai maman Sagir cututtuka sunyi yawa ba sai mutum yana wani tunani ba Allah dai ya sauwake ya juya zai fita sai ga a Alhj ya turo kofa yayanmu ya matsa Alhj ya shigo yana ma mama bayani sun tabbatar da zuciyata na son ta harbu sannan yace su tuhumeni ko akwai wanda takeso ne ko abinda ya shafi haka yayanmu yace Alhj bari nima na ganshi likitan sukace to lokacin Alhj yasa an tashe ni zaune ni kaina nasan na rame sosai cikin kwana daya yayanmu ya dubeni yace sorry Iman na dubeshi yaune na fara jin ya kirani da Iman na daga kai alamar amsawa,yace maman Sagir me taci?mama tace bata ci komi ba yanzu ne dai zan hada mata to amma tace sai tayi sallah tukunna,ya dubeni zaki iya yin sallar ne?nace eh tare da taimakon mama nayi alwala muna fitowa daga bayi yayanmu yayi mana sallama yace da daddare zai dawo haka na cigaba da jinya har tsawon kwana uku kullum yan dubiya suna zuwa,Amira da Mami nan suke yini haka yayanmu da yaya Kabir nan sau uku suke zuwa sai dai duk lokacin da yayanmu yaga yaya Kabir haushinshi yake ji, gudun fadan alhj yasa kishiyoyin mama suka zo sau daya kuma basu kawo mana abinci sai dai anty Yagana da maman su Amira kayan ciye ciye kam yayanmu ya kashe kudi har Anty Mimi ya kawo ta gaisheni nasan dai dole tazo ba don son ranta ba,niko ban ma ji wani dadin zuwanta ba don ma kadan ya rage ciwona ya dawo musamman ma da naga sun sa anko yellow kampala sun man kyau sai dai kishi da ya sani gaba,ban san yanda akayi su yaya Abubkr sukaji ba sai dai ganinsu nayi yaya Ibrahim ne yake ce min babana yana nan zuwa,yace a gaisheni naji dadi har ina tambayarshi yaushe zaizo?yace kilan yau ko gobe nace kilan a sallame ni yau ai a ranar aka sallameni kafin sati na dan girgije,yan skull dinmu na comp ma sun zo duba ni randa na cika kwana goma ranar na koma zuwa makaranta lokacin saura kwana hudu bikin yayanmu su Mimi duk sun damu da bikin sai rawar kai suke yi har Mami na cewa da ban warke ba bikin ba zai mata dadi ba sannan suna son kudi gun yayanmu nice ma zan amsar musu nace ke Mami ki rabu dani ba wani kudin da zan tambaya a raina nace in baku san dan dole zan zauna a garin nan ayi biki ina nan ba da ba dan mama ba zata yarda ba da naje tudun wada gidan kawuna sai angama sai na dawoa dare yayanmu ya aiko nazo lokacin ina zaune a falo ni da mama tana nuna min memo data buga da sunansu au Jamila da Sagir sai agogon bango suma guda dari wai in bashi ince ni na buga na dauki guda daya ina dubawa hotunansu ne sunyi kyau sosai na hadiye wani abu da yazo min wuya na dubi mama nace sunyi kyau amma kin sha kudi tace yaya za'ayi ai yana da mutunci sosai Abdulrahim na ce umm waya baki hoton su?tace gun Kabir na amsa na rike hawayen idona lokacin da naga sunana a matsayin wacce ta buga kafin nace wani abu ne jamila ta shigo anty Iman kizo inji yayanmu na danyi tsaki nace kice kaina na min ciwo ba zan iya zuwa ba a raina nace ba zanzo ba tunda ka kama matarka a hannu kasata aikin,Mama ta dubeni kije mana Iman kije mishi da agogunan nace banjin dadi ne mama tace daure na mike na ciccibe kwalin agogunan na ce bari na kai wannan sai na kuma zuwa na dauki dayan da kyar nakai dakin nayi sallama na shiga yana zaune da kaya a gabanshi fuskarshi babu walwala ya dago kai ya dube ni yaya kai din na dan lumshe ido sannna nace da sauki na kula tun da nayi rashin lfy sam baya son yimin tsawa ko fada ya dubi kwalin dake gabana yace menene wannan?mYaya gudummuwata kenan a ba jama'a. Ina zuwa na koma na dauko dayan kwalin na samehi yana duba wa ya dubeni yace amma sunyi kyau mun gode,na danyi yake nace um ya turo min kayan gabanshi yace ga naki kayan bikin harda ankon,nace ai Baba yayi mana ankon,yace duk da haka ki dauka ina son ki kaima telanki da yake maki dinki don ya iya sosai nace yaya Sulaiman ne ya ma samu aiki yanzu bai cika zaman shagon ba sai dai yaranshi,yace to kikai inda za'ayi maki mai kyau,takalman ki jakunkuna sai yau za'a kawo anjima kadan gidan Nasir na manta su nace na gode ya kuma duban hannuna ke bakiyi lallen bane?nace eh yace kiyi gobe zanzo na kaiki saloon mamaki ya kamani nace ko dai yana zaton da Amaryar yake magana ne?ni da ban taba shiga motar shi ba,na boye mamakina nace ai bana sa relaxer kitso nakeyi yace to kiyi kitson kinji ni?nace to.kaya ne kala shida less biyu super biyu sai material daya sai shadda,shaddar din kakkiya ce ta sha aiki riga da zani sitayal din ya hadu ga shaddar mai tsada,turare kala uku masu kyau da mayukan shafawa sai sarka da 'yan kunne,Mama ta dubeni tace oh ni Habiba wannan hidima tayi yawa, shida ke cikin biki kayan nan Iman ba'a karbe su duka ba bani wayata gata can a chargy,na dauko mata shi ta kira tana mishi korafin yawan kayan bansan me ya ce mata ba naga tayi murmushi tace ai kanwarka ce kowane ai ta maka kabiyata kenan?can kuma tace to shi kenan an gode Allah yasa ayi wannan biki lfy ya kuma bada zaman lfy.Washe gari na shirya sai tudun wada na kai dinkunan a can nayo kitsona da lallen filawa mai ratsin ja,gidansu Amira na biya tace min zakije Arabian day din ne yau?nace Mami tay min magana amma da kyar in zani kinsan bana shiri da Amaryar, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Amira tace indai ba zakije ba nima ba zani ba dama domin ke zani nace to bari in zani zan maki waya ba karfe hudu bane?na duba lokaci a wayata karfe biyu da minti arbain nace bari na shiga gida dama dinki nakai tudun wada,Amira ta dubeni tace name kuma ba kinyi anko ba?nace jiya yayanmu yace ga nawa ankon dana duba sai naga ba anko bane ya dai minne ne kala shida harda takalma yau da safe ya bani takalman kala uku,Amira tace gsky jininku ya hadu,sanda baki da lafiyannan kar ki ga yanda ya damu ba dan munsan yanayin rayuwar shi kenan yin alkhairi ba damin zargi ko sonki yake na kai mata duka nace me zukekiyar mace kamar Mimi me zaiyi dani?Amira tace Iman kina da kyau amma sihirtacce ne sai na kusa dake komai sonki ko kuma yasan kyau zai gane kiga Mimi mai mata kallon gane muni zai ga muninta don tana da goshi da kuma....na katse ta mu bar zancan nima ai in an kura min ido za'a ga muni nawa,Amira tace Allah baza'a gani ba sannan ne ma za'a ga kyaun ki nace um bari na shiga gida. A gurin Arabian day kowa yayi kyau Amarya cikin jallabiya baka da dan hijabi tana zaune a gun da aka tanadar mata muka shigo nima sanye nake cikin Jallabiya mai hawa biyu baka da ja hijabina da takalmina jajaye ne, Hijabin dan karami iya wuya su mami da Anty Mariya da kawayenau sai kai kawo suke ni kam guri guda na kame mai kyamarar sai daukata yake tamkar nice Amarya,ga masu Hotuna,Amira tace kai Iman kin tafi da imanin masu hoton nan sai ke suke dauka kafi n inyi magana Bilkisu tazo tace kai bafa wannan bace Amaryar ba kun ganta tayi maku kama da Amare?nan suka juya suna daukar ko ina haka taro ya tashi lfy ba tashin hankali,washe gari sister day da safe yayanmu ya aiko nazo dakinshi na same shi ya dubeni me kike yanzu?nace ba komai yace to abokaina ne na england yau zasu iso ina sonki shirya masu abinci kaloli masu dadi don gidan Nasir zan saukesu kamar nawa ake bukata?ko muje kasuwar tare in yaso sai ki duba abubuwan da zakiyi amfani dasu gaba daya a wajen girkin?nace to bari na sanar da mama yace shima bari yayi wanka,cikin riga da wando na material ruwan madara da filawoyi jajaye dan hijabina dan karami sai takalmi sai abinda ya kamata na siya da kulolin girkin da zan masu har da na sha ina tsaye jikin motarshi ya fito daki sai da ya shiga su Sa'a da Bikisu da Maryam kanwar anty Mimi dukkansu ni suka tsura ma ido na shige mukayi gaba,ba wani hira muka yi ba ya dai sa wakar tashi dakusan duk kullum sai naji ta a dakinshi tun ina jin haushin wakar har yanzu nima ina sonta kuma nama sai album din wakokin mata celine dion ina wakokin don sanyin muryarta,wayata ta soma kidan kuch kuch hota hai na kai hannu zan dauka sai naga yayanmu ya dafa wayar ya dauka ya duba sunan Amira ya gani sai ya mika min nayi ajiyar zuciya sannan na amsa hello,Amira yaya dai?tace kina ina ne?nace muna hanyar kasuwa ne menene?tace na sha kina gida ne na shigo,nace bana gida in na dawo zan shigo gidan muyi aikin abincin baki tace to sai kin dawo. Sayayya mai yawa mukayi komai nace biyu sai yace na dau uku,gidansu Amira ya saukeni ta fito muka kwashe kayan,mun shirya abinci kala kala dana sha a sabbabin kulolin da muka siya muka shirya muna gamawa muka yi wanka na shiga kenan don nasa kaya yayanmu ya kira ni nazo yace kun gama?nace eh yace to ga musa dryva nan ya kaiki gidan Nasir ni kuma zamuje mu dibo su sauran minti biyar su shigo KD daga Lagos nace to,banyi wani shafe shafe ba nasa atamfa charas babba riga da siket ne dinkin shot play sai karamin gyale muka jera abincin nace Amira tazo muje tace aah ba ruwana da wannan yayan naku zai iya kado ni,nayi dariya nace shi kenan,nayi kusan minti talatin da zuwa sannan suka iso cikin harshen turanci suke magana nima na gaishesu cikin yaren nasara,Nasir yace ko inyiwa Mami waya ne tazo ta taya yarinyar ne?ya harareshi yace ban ce ba nikuma bayan sun zauna na gabatar masu da kayan ciye ciye da shaye shaye na gida dana company,wani shima bakin fata ne duk sanda na dubeshi sai mun hada ido dashi haushinsa ya kamani can kuma wani daga cikinsu yace Maska wannan itace Amaryar?yace a'a ita kanwata ce sai yace to zaka bani kanwarka?don tana da kalar asalin yan Nigeria yayanmu ya daure yace baya son wannan maganar bakin fatar dake kallona yace Maska ni zaka ba wannan mai kyaun din,don bana neman wata kasani,y hiayanmu bai kuma magana ba ya dubi Nasir yace bari na kaita gida na dawo,ya dubeni tashi muje na dube su nayi musu sallama, a mota yace in zaki fita ki daina shafe shafen nan na dubeahi nace ban shafa komi ba sai hoda,yace duk inda kikaje sai ance mun ana sonki ni kuma krt nake son kiyi ni dai nayi shiru yace kin tuna alkawarin da kikayi min ko?nace eh yace to kar ki yarda ki yi wasa da cika alkawari kin jini?nace e.A kurarren lokaci muka isa gun Sisters day Angoma bai zoba na tambayi Mami tace min yayi ma Amarya waya yana tare da baki muka zauna,nanma ba laifi bikin yayi kyau ranar ne akayi sa lalle banje ba, washe gari lunching a hamdala hotel za'ayi sanye nake cikin dogayen riga na shiga dakin yaynmu dan amsa kkranshi yace zauna na zauna a kasan carpet ya dubeni yace yau wane kayan zakisa,nace anko zamu sa yace to kar kisashi kisa sky blue din less din nan,na gama kanki ba tare da wani tunani ba na zame dan kwalin kaina kananan kitso ne 2step mai zigzag,yace to rufe ki shirya sosai ya dubi dakinshi yace ga kayana nan dukkan abinda kike so ki dauka na baki ki dauka nayi shiru na sunkuyar da kaina ya taso ya tsugunna gabana Aminatu ya kira ni a hankali cikin sanyin nan nashi na dube shi nidai da zance frame din nan nake so amma sai nayi shiru ya kuma kiran sunana na dube shi

Chapter 6 of 7