Share this page
2 / 7
ne shiko yaya Ibrahim dan Baba Auwal ne(wato dan kishiyar kakata)tun kan a haifeni suke gidanmu kuma suna makarantar gumi college SS2 don haka tare muke zuwa hutu kauye dasu,kuma muna kama dasu don duk wanda ya ganmu yasan yan uwa ne saboda kokarina a kai ta turanni gaba a makaranta sannan kusan kowanne malami ya sanni don haka ina da shekaru goma sha daya na kammala primary din tare kyaututuka masu yawa muna zaman jiran fitowar sunayenmu ne,na fuskanci matsala ta soma kunnowa gidanmu in da mama ta tada hankalinta ni ban san dalili ba amma nasan nasha ganinta tana kuka in nace mama menene?sai tace idonta ke ciwo kuma koda yaushe zanga anty yagana kawar mama tana zuwa gidan su shiga daki da mama suna yan shawarwari,ni bansani ba wai ashe baba ne zaiyi aure da wata banufiya mai suna fati kuma ance ma mama bata da mutunci shine hankalin mama ya tashi tace da baba gsky ya canza mata sai baba yace karyar mutane ce kawai ya dinga lallashi gami da ban baki sannan ya kara mata jari har na naira dubu dari takwas dama tuni ya sai mata motocin bus guda biyu da babura ana mata haya dasu,anty yagana makociyarmu ce yar asalin maiduguri ce amma zama ya kawo yayarta da mijin yar in da suke zaune kurmin mashi yayarta ce ta aurar da ita ga wanda take so Alh shu'aibu ma'aikaci ne a water board, tana da yara ukku kusan tare aka haifemu da yarta ta fari mai suna saudatu,suna amintaka da mama sosai haka ni da sa'adatu makarantarmu daya,bayan haifuwarmu ne anty yagana ta kara haifuwar yara biyu Nurfa da abida,Mama ko shiru tun daga kaina,anty yagana itace ta ba mama shawarar su hada jari su soma harkar yan kunnen gwal da jallabiya da zannuwan gado suna bada sako ta hannun wani abokin Alh Shuabu ne mai suna Alh Mukhtar Maska Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Dan zinare ne a kasuwar sheikh Abubakar gumi yana da shagunan jallabiya da gwala gwalai,shine yake kawo masu kaya in ya fita dubai harka ta amsu don da an kawo xaka ga matan manya suna zuwa suna dubawa suna saya don haka mama ta cire hankalinta daga batun auren baba,bayan auren amarya Fatima ta tare a dakinta da farko ta kwantar da kai amma ganin yadda mama ke facaka da kudi yanda baba ke ji dani sai hankalinta ya tashi ta shiga tsiro fitintunu iri iri yau tace kaza gobe tace kaza tasa su yaya Ibrahim da yaya Abubaar a gaba,a nan mama ta taka mata birki tace kar ta sake ta takura masu suma gidan ubansu ne in tana jin masifar tata ta yi da wanda ya ajiye ta bada yara ba,wannan rigima har gun baba jin bata sami gsky ba shi ne tayi yaji sai da tayi wata sannan ta dawo,dawowarta shine ya zama sanadin juya mana baya duk yanda baba yayi sam baya sauraron mama da farko ban gane ba saida sunanmu ya fito munci makarantar mu salmat da mama ta sanar da baba sai yace kar mu dameshi ya gaji da biyan kudin makaranta,ni ba wani kokari ba shi maimuna gwarzo zai maida ni na ringa kuka ina rokonshi sai ce min yayi inyi hakuri shi ya gaji,haka na cigaba da zuwa islamiya da hadda boko kam ina ganin saudat tuni har ta shiga SS1 niko ina gida ,anty yagana tace da mama ta biya mani da ita tana da kudi tace ai ta mashi magana yace bai yarda ba,wata rana na dawo daga hadda da rana jugum na samu mama tayi a dole na zauna kusa da ita na dafa ta nace wai mama baki da lafy ne?tace kaina ke min ciwo iman,na tashi na nufi gun da muke aje magunguna na dakko mata panadol na dibo ruwa a kofi na kawo mata ta amsa tasha sannan tace kije dakin yayan ki duk wanda kika gani cikinsu kice yazo zan aikeshi wajen kawunku malam nace nima zanje mama tace to amma sai kinci abinci ko?nace e nayi sashen su yaya da gudu,a kofar dakinsu na tsaya nayi sallama yaya Abubakar shine ya amsa nace in shigo?yace in dai tsohuwa ce kar na ganta anan(haka su kan tsokane ni wai tsohuwa)na shiga nace kaine dai tsoho bani ba yace me yasa zaki sa mana tsufa daki don Allah kije waje nace naki din aje wajen baka girmeni ba ma zaka ce min tsohuwa,ya kwashe da dariya yace waneni da girmanki kece fa kika haifi su kawu da mama da baba anan gidan haushi ya kamani na hau tsaki irin na shagwaba ina son inyi kuka nace sai na gaya ma mama na juya zan fita ya jawo ni zo mana yar kanwata tawan zo mana kiji mama ta aiko ki guna ne?nace eh tace kazo zata aikemu gidan kawu malam ya mike ya dungureni shine baki fadi mani tun dazu ba?ya rike min hannu muka tafi dakin mama ban san me tace mashi ba na dai ga ta bashi kudi sanna tace in tafi falo inci abinci kafin ta gama bashi sakon,na kunna tv na kamo cartoon ntwk ina kallo ina cin abinci sai naga anty Faty ta fito ni ban ma ganta ba sai gani nayi an kashe tv din na dube ta nace aunty ina kallon tom and jerry ne,tace na kashe ko zaki kunna ne?niko ban san gatse ba sai nace eh cikin masifa tace to zo ki kunna har ga Allah ni ban san gatse tai min ba sai kawai na tashi na kunna tv din remote din na hannunta kafin na juyo sai saukar mari naji dau na yanke da ihu sai ga mama da gudu ita da yaya Abubakar dama shi akwai shi da zuciya yace faty me tayi maki,anty faty tace in dole sai kasan abin da tayi min to ka nemi sani daga gareta dube ka dan kauye don kazo ka waye shine zaka kawo mana raini ko?yace naji ni dan kauye ne ke baa ma san asalin naku kauyan ba,don ba muga yanuwanki ba waya sani ma ko daga sama kika fado banza yar iska haka zaki kare a neman asiri,sai tayi kanshi da zagi harda duka nan da nan ya sharara mata mari gami da ture ta mama da tuntuni take tsaye tace kai Abubakar wuce kasai kabar aiken sai anjima,ta nuna ni ke kyma yi daki na mike sannan na jiyo mama tana cewa kin gani ko faty wannan shine abinda na jima ina sanar dake ki daina shige ma yarannan kinki ji to kinga irin.......kan mama ta karasa sai ta katse mata hanzari da masifa ke munafuka bake kika sasu ba?to albishirinki yau dinnan zaki san matsayi na bakinsa Abubakar ya mareni ba?zaku gane baku da wayo yau,nayi shiru a daki ina kuka mama tace to ina jiranki da alkhairi anty Faty tace ni kuma da sharri nake jiranki yau da nai nasarar rava alkhairi da tunanin wata ya mace haka zan rabaku da gidan nan mama ta ce to ai Allah ya fiki kuma ba ya barci kuma yana tare da masu hakuri ta cigaba da cewa ke ko nasan baki san haka ba tunda kin yi nisa ba zaki taba jin kira ba to sai muce Allah ya shiga tsakaninmu da ke in kuma mai shiryuwa ce Allah ya shiryaki,Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 ta shigo ta sameni inata faman kuka ta zauna kusa dani ta jawo ni jikinta tace iman wace adduar kike min,nace ina rokon Allah yasa ki daina samun matsala da baba,mama tace ki hada da babanki shima ki dinga yi mishi ki roki Allah ya kareshi sannan ya raba shi da dukkan sharri da ake mashi,nace mama wanene yake ma baba sharri?tace aa mugun abu ai ba sai kasan me maka zaka roki Allah ba,nace to insha Allahu zan dinga yi mishi,da dare sai ga dan aiken baba,yaya Ibrahim ne baba ya aiko wai muzo ni da mama babban falo babu neman ba'asi ya dauki hannu a gaban mutane ya mari mama ga yan aiki ga yayyena ga ni ga anty faty bayan marin ya cigaba da fada wai kar ya kuma jin an taba mishi mata inko ta kuma marinta ta mari aurenta mama tana rike da kumatu sai nan tace cewa tayi maka na mareta?yace to yau kuke me yasa tun da kuke tare bata ce kin mare ta ba sai yau kuma tace tana son in rama mata shi yasa mama tace shi kenan ni Allah ya rama mani ta shige daki,duk da karancin shekaru na sai da nayi mamakin baba wai ya rama wa anty mari?na juya na dubi anty sai naga tana wani ciccika tana batsewa wai an rama mata, na bi mama daki na iske tana kuka na dafa ta nima na soma kuka ina cewa mama kiyi hakuri Allah ya saka maki. Anyi haka da kwana biyu na dawo daga kitso in da yaya Abubakar ya kaini tudun wada na mari yaya Abubakr din da wasa don ya dameni da tsokana tun a mota wai tsohuwa mai dan koko Allah kashe ki musha gumba,nayi banza dashi sai da ya tsaida mota sannan na dan kai mashi marin wasa kadan na bude motar nayi cikin gida da gudu,yace ni kika mara?sai na rama shima ya fito yana dariya ya biyoni yana kirana nayi falo da gudu ina cewa so kake in tsaya ka rama ban kula ba na bude labulen falon na fada sai kawai naji na bige mutum lokaci guda kuma naji anyi jifa dani ashe nayi karo da anty faty ne shine ta jefar dani kuma ta biyoni da duka takeyi yaya da har ya juya da yaga na shige falo sai kuma yaji kukana nan da nan ya dawo ya iske anty nata faman dukana cikin zafin rai yake ma anty magana yace don Allah me yarinyar nan ta yi maki kike dukanta haka?yanzun nan fa muka shigo?ta juyo kanshi da zagi da gori,jin hayaniga shi yasa mama ta fito ta dubeni ta dubi yaya sannan tace Abubakr ba zaku daina daukar min magana ba ko?yaya yace wllh mama bamuyi mata komi ba niko sai faman kuka nake ita ko anty faty sai zage zagenta takeyi jin mama bata kula ta ba sai kawai ta shaki kwalar rigar mama tana cewa yau din nan na tsara zaki bar gidan nan duk na cinki miji ya wulakanta ki amma don bakin naci kin dage kin ki tafiya ko,ta cigaba da cewa to yau din nan za'a kama kai a koma wurin mai dattin hula,yaya ya fincike hannunta a wuyan mama sannan ya daura mata mari yace marar mutunci yar dangin jaraba rigima dai ta ki karewa har yamma sai da tayi ma babana aike har kasuwa wai yazo nan da nan sai gashi lokacin ma kowa ya kama gabanshi yaya Abubkr bai ma nan ni kuma ina daki mama tana koya mani karatu sai ganin baba mukayi ya shigo ko sallama babu ya jawo ni a gaban mama ya hau duka da wayar wuta ina ta ihu gami da neman taimaki amma ina mama ko kallo ban isheta ba sai da ya gaji sannan ya barni don kanshi,sannan ya dubi mam yace ke kuma in tambayrki?mama ta dubeshi ba tare da tayi magana ba yace dake muka hada muka sayi gidan nan?mama tayi shiru yace ba dake nake magana ba mama tace ai ina jinka yace to ina son daga yau na sakeki saki daya sannan na barki minti goma ki barmin gidana.....Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Duk da nike karama ina jin ya ambaci saki sai na kara yanka ihu itako mama duk da dauriya da tayi don kar tayi kuka ace gabana sai da kuka na ya sata hawaye koda mama ta gama kimtsa kayan ta ta fito falo zata tafi na biyo ta da gudu ina kuka babana yana zaune yana cin abinci da bai tanka ba sai da anty tayi mashi wata magana sai yace da mama ki tafi da yarki in kinji shawarata don ni ynxu nafi son yaya maza daga tsatson faty ga mamakina sai naji mama tace to Allah ya baku sannan na gode da shawara amma ko mun tafi da iman ai kanan nan a matsayin ubanta ko?maimakon yayi magana sai kawai ya kalli anty faty komi tace mashi oho sai ya juyo ya kalli mama yace kuje dai sai yanda hali yayi idan nine ubanta to na aiko maki amma fa gunki zata ci gaba da zama ba ba tare da mam tayi magana ba ta jani ko takalmi babu mukayi waje,wannan fita da mukayi itace fita ta karshe daga gidan babana mahaifi kuma har yau ban kuma zuwa ba ban kuma ganin babana ba ko anty fati ba. Muka koma gidan kawuna marikin mamana daki guda kato bayan sati biyu babana ya aiko ma mama da dukkan kayanta haka mama ta cigaba da zaman iddarta har ta gama, itace tayi mani komi na shiga SS1 a makarantarmu wato salma,ina jin dadin zama da baba uwa wato matar kawuna suna da yay biyar yaya suleiman shine babba sai yaya nura,anty rukayya ke binshi sannan sai nana itace sa'ata sai karamin su mai sunan kakanmu liman ake kiranshi don sunan liman din yaci wato isuhu,nana maimuna gwarO take itama js1,yaya suleiman tela ne kuma yana zuwa poly ko da yake san da muke a maigidansu saura yan kwanaki ya gama shi ko yaya ustaz ne don yanzu haka ya na koyarwa a wata islamiya nan kusa da gidansu,sannan shima zuwa tashi wato sanawiyya a unguwar ma'azu,anty rukayya kuma tana aure ne a badarawa yaya suleiman yana debe mani kewar su yaya Abubakar don shima yana tsokanata kasancewar mu abokan wasa ne ya kance mani matar ni kuma ince mashi ya mani tsufa bana sonshi yaya nura baida faraa shiya sa nima ban cika kulashi ba,Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 wata rana ina zaune daki sai mama ta shigo lokacin kuma gab da babbar sallah ne mama tace iman shirya muje kasuwa nace to dama na riga nayi wanka sai kawai na dauki hijabina mai less a kasanshi nasa takalmina nace mama na shirya muka nufi kasuwa,bayan mama ta gama mana yan saye sayenmu nida nana sai tace muje wajen yan zinari zata sai wani nace to muka je shagon shi makare da gwala gwalai kala kala da fara'arshi ya tari mama,naji yana cewa haj Habiba sai yau kikazo kasuwa?mama tace wllh ko Alh mukhtar maska inafa son nazo amma ban samu lokaci bane sai yau ya turo mana kujera yace mu zauna ya nunani yace wannan yarki ce ko?mama tace aa yace ke yarta ce ko yan mata?nayi murmushi yace ga murmushin nan irin naki ke ya sunanki?nace sunana iman yace suna mai dadi,sannan ya juya gun mama yace kin sami sakona a gun yagana? don tazo shekaranjiya ta kawo wasu karyayyun yan kunne,mama tace bamu hadu ba gsky mun dai rabu akan zata zo nan din yace sakona bai isa ba kenan?mama tace eh sai ya dubeta ya ce zaki samu ganina zuwa yaushe?sai nazo gidan naku,mama tace lafy dai ko?yace sai alheri mama tace to ko yaushe kaxo zaka sameni sai dai da safe ina zuwa islamiya yace ba matsala zan shigo tudun wadan yanzu me kike so?mama tace ina son in saima Iman dubai ne kasan da na daukar mata a cikin kayan da ka kawo mana wancan sati ukkun da suka wuce to sai na ga kuma sun mata girma sai naba yagana tace kace mata sai bayan sallah shine nace bari nazo gunka ko zan samu wani,yace ba zaa rasa ba in kuma kinga ba wanda yayi miki to ki sai mata saudiyya mama ta zabar kirar dubai na wajen dubu tamanin har da abin hannu guda biyu yace gasky kina ji da wannan yar taki mama tace kai maska don na sai mata yan kunne?yana dariya yace sai nazo zan amshi kudin mam tace a'ah ga dubu hamsin nan bansan zan sami masu tsada haka ba mukayi sallama ya bani dubu daya yan hamsin hamsin a cikin kudin nayi godiya muka tafi,bani manta ana jajibir sallah Alh mukhtar maska yazo gun mama ni dai na dawo daga kitson sallah nida Nana na iske bako a dakin yaya suleiman da zai tafi mama ta shigo tace naje na gaida shi don yana ta faman magana in na shigo nazo mu gaisa,na zauna a kasa dashi na gaishe ahi yace kin dawo muga kitson na nuna mishi yace iyye yayi kyau sosai yasa hannu a cikin aljihun shi ya dauko kudi sababbi yan naira ashirin bandir daya yace ga goron sallah don kilan ba zaki ganni ba naki karba nace ka barshi muna musu mama ta shigo jin musun da mu ke ne tace sunyi yawa ne alhaji ka rage yaki dole na amsa nayi godiya.Amira wacce tayi shiru tun da na soma magana kamar ruwa ya cita sai da nayi shiru sannan tace gsky iman ke yar gata ce to amma sai nan gaba zaki sani in Allah ya kawo karshen muguwar matar babanki,nace Allah yasa,Amira ta gyara zama sannan tace anty faty matar babanki ta haihu?nace kai har yanzu Allah bai basu ba tace to ina yayyenki Abubakar da Ibrahim kuma?yanzu basa zuwa nan?nayi murmushi nace kin cika tambaya Amira zaki yi kyau da yar aikin da nake ra'ayi wato yar jarida Amira ta basar da abunda nace tace baki amsa mani ba nace basu san nan gidan ba don kwanaki baba uwa tace masu mama tayi aure,sai kuma ta kuma cewa to ina yayansu mami abdul wa ma kika ce mani?nace abdulrahim sunanshi mami tace yana england shi dan wasan kwallo ne nima ban sanshi ba amma ya sha masu aike nima na gani,shi kuma kabir aikinsa shi dai amira tace haba nasan shi mana ba shi ne yake karatu a kano ba,tace ai shi naga ba ruwanshi don naga yana maki wasa nace gsky shi kam ba ruwan shi ko zai zo hutune ya kanzo da yar tsaraba su sweet biskit da yan kayan lashe lashe ya ba kannenshi tonima yanda ya basu haka yake bani don haka nima nake sonshi a raina ganin shi nake kamar yaya abubakar duk da bai tsokanata irin na yaya abubakar din amma kinga yayan nasu da ke waje ina tsoron ranar da zai dawo,ta dube ni don mi kika ce haka?nace don ina jin yanda suke lbr shi wai ya cika masifa ga duka sannan nasha jin yanda suke bada lbr irin son da yake ma hajiya yaya,sunce yana son mamarsa kamar ransa don bai hada ta da kowa ba yanda mami take bada lbr sai kinyi mamaki sosai abin kamar ba gaske ba to kuwa ai kinsan dole ne ya kuma ki duk abunda taki gami da tsanar shi tunda sunce komi tace mashi yayi,don haka ina jin ance yau zai dawo zan hada ya nawa yanawa na kama gabana na koma can gidan kawu na malam,Amira ta dinga man dariya wai na cika shegen tsoro nace ai ke dariya ma nabaki?lallai Amira, tana dariya tace dole ne nai maki dariya ma naga dai komai son uwar shi sai kin mata abu sannan zata sanar dashi sannan in baki sani ba su maza ba yawancinsu basu da daukar zance na tsegumi haka wannan sai mata sai ko sakaran namiji ina jin wannan ba zai maki haka ba don shi dan boko ne nayi shiru ina nazarin maganarta can nace wannan gasky ne to Allah yasa dai kar ya kulani,Amira tace amin,mun kaure munata zuba lbr sai kawai ganin yaya Ahmed mukayi nace a'a yayanmu ustazi ba sallama ne?yace ku dai bakujin sallamar to mama tace a tashi ayi sallah dama masallaci zani,yasa kai ya yi waje na mike nace bari na wuce gida kawai,Amira tace ai baki isa ba sai kinyi sallah kinci abinci sannan zaki bar gidan nan,na kwace daga riko da tai min nayi waje ina dariya nace yaushe rabon da ki shigo gidanmu,ta biyo tana kira na gudu gashi nayi sa'a mamansu tana daki tana sallah a gidanmu ma mamanmu sallah na sameta tanayinima sai na shige dakinmu naga jamila tana barci na tashe ta muka yi alwala muna idar da sallah nima na kishingide. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 DOCUMENT CREATED BY ZAHARADDEEN SHOMAR WHATSAPP ,08168575100 Tawa Tasameni1-02 Posted by ANaM Dorayi on 01:20 AM, 20-Dec-15 Under: TAWA TASAMENI TAWA TA SAMENI NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Ranar lahdi da daddare sai gasu yaya abubakr sunzo nan muka sha fira, ynxu anty faty ta gama mallake babana sai abinda tace gashi har ynxu Allah bai basu haifuwa ba sai karyar bari,na tausaya ma mahaifina kuma na yi alkawarin sa shi a addua insha Allahu zan kuma roki mama ta barni inje na gaida kakata in munyi hutu mun jima dasu sannan sukayi sallama damu suka tafii,muna shirye shiryen soma jarabawa zango na ukku don shiga SS2 aka yaye mu a islamiya inda mukayi walima a gidansu Amira duk gidanmu ni kadai nayi sauka mami kuma sai shekara mai zuwa don tayi wasa da karatun mama da maman su Amira harda Anty yagana duk sun mana bige bigen abubuwa irin su kalanda da robobi,hankici da sauransu,da zamuyi rabon katin walimar har su yaya Abubkr sai dana bawa Amira nayi mata kwatancen taje takai masu kuma sunxo mani da kyautututukan su inda suka bani waya a kwalinta wai inji babana na amsa cikin fargaba na kai dakin kwananmu na boye shima yaya Sulaiman yazo kuma shine ya dinko mana kayan da muka sa ranar walima nashi gudummuwar kenan wata shadda ce galila mai kyau da hijabai. Sai da komai ya natsa sannan na dauko wayar dasu yaya suka bani na kai ma mama na mika mata leda ta amsa ta gami da tambayar menene a ciki?nace su yaya Abubkr ne suka kawo wai inji babana na fada mata cikin tsoro,ta saki ledar daga tsaye tace ke kuma ki ka amsa to ko menene ma a ciki zan maida musu ni,haka kuwa akayi ta kira yaya Abubkr a waya ta bashi gami da yi mishi gargadin karta kuma ganin wani sako daga babana da sunan wai nawa ne tun daga nan suma su yaya Abubkr din ta daina sakar masu fuska.mun shiga SS2 cikin sa'a da nasara ranar wata jumaa mun tashi daga makaranata na tsaya ina amsar sakon wani littafi da zan amsar ma Amira gun wata yar ajinmu Hauwa aminu don yanxu in tana karantawa nakan zauna ta bani lbr ko ta karanta mani na amsa na isa gurin da Musa yake tsayawa wato direbanmu ban sameshi ba na tsaya nayi sororo can na hango wata yar ajinsu mami don yanxu ba aji daya muke dasu ba ni ina A su suna C na isa gunta sai na tambayeta ko taga su Sa'a?don mami bata zo ba tace mani sun tafi abinsu nayi shiru na kuma ce mata motar tazo?tace ba bus din gidanku ba?na daga kai tace to sun dade da tfy,sai da nayi nisa a tfy kasa sannan wani tunani yaxo mani na tsaida mashin na hau sai da muka zo har kofar gate din mu sannan nace bari na shiga na amso maka kudinka ina shiga harabar gidanmu naga matasan layinmu sun cika a kofar dakin yaya Kabir har da wadanda ban taba ganinsu a layinmu ba,nace a raina ko yaya Kabir ya dawo ne?don ynxu yana bautar kasa ce a Bayelsa na shiga gida na sanar da mama abinda ya faru tace to a nawa ya kawoki?nace 40,ta bani 50na kai mashi a hanyar dawowa cikin gida ne nayi karo da Anty Hadiza dasu Anty Mariya suna dauke da manyan tururuka da kuloli a kai,Bilkisu kuma tana dauke da dauke da plates da cokula ga wani kwando mai dauke da kayan shaye shaye na dube au na kauce a hanya,amma duk da haka sai da anty Mariya ta daka min tsawa ke akuya ban hanya,na matsa musu suka wuce,na shiga ina mamakin wane bako ne yaxo ake mashi hidima haka?bayan naci abinci nayi wanka nayi sallah na shirya cikin riga da siket yan kanti ina zaune a tsakar daki ina yin note sai ga mami da gudu ta shigo tana kwala min kira iman! iman!!na tashi da sauri ina fadin gani nan nace menene?don duk na tsorata sai tace min ki tayamu murna yayanmu ne ya dawo ya bamu waya nayi ajiyar zucya na dungure mata kai nace har kinsa duk na tsorata na amshi wayar kirar nokia yar karama mai murfi gsky ta burgeni sosai nayi mata murna tace su dasu Sa'a iri daya ya sai masu don dama ya sai ma su anty Mariya tun tuni,nace kunji dadin wllh tace muje ku gaisa mana ko zai baki kema na dube ta cikin sauri nace ki rufa mani asiri ai ni ynxu ba zan taba yarda ya ganni ba bare da hankalin kaina naje inda yake ta soma dariya gami da fadin kin fiye tsoro me zaiyi maki?daga ganinki sai ya hau dukanki sai kace mahaukaci?tacigaba da dariya na ture littafin gabana na dube ta nace don Allah ki sanar dani wani abu game da yayanmu mana, Tace Abdulrahim sunanshi na gasky wato Abdulrahim mukhtar maska a yanda naji ana cewa tun yana dan karamin shi sam baida yawan fara'a ga miskilanci don zai iya kwana bai damu da yayi ma wani magana ba in ana son aga fara'arshi to a bashi kwallo sannan kwallonshi ta samo asali ne tun yana makarantar primary inda yayi ta cin gasar da aka sha hada su da wasu makarantun,haka yacigaba har secondary,bayan kammala yaso a barshi yaci gaba da kwallonshi amma sai babanmu ya kiya sam dole yaje ABU zaria inda ya karanci politics har ya samu degree bayan ya gama sai ya shawo kan babanmu da kyar yayi wasanni da dama a nan gida nigeria kafin ya fita england inda wani coach yayi mishi hanya, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Na dakatar da ita nace ke ni ban tambayeki lbr kwallo ba,kunce yana dukanku ko?mami tace Allah yana duka sosai ma,amma sai ka mashi ba daidaiba,na dubeta nace kamar yaya ba daidaiba?tace baya son ya saka abu kaki ko kai shirme,bai son kazanta kuma in ka ganshi yana son ka gaisheshi amma baison yawan gaisuwa ,kana ce mashi ina kwana is ok,yana da cin abinci kinsan yan kwallo gashi da tsafta yana son kamshi ke gadai abubuwa

Chapter 2 of 7